Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sabuwar Dama Ga Masu Zaɓe: INEC Ta Tsawaita CVR Zuwa Ƙarshen Yuli
Published: July 7, 2026 at 3:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa a Najeriya wato (INEC) ta sanar da tsawaita aikin Rijistar Masu Zaɓe (Continuous Voter Registration CVR) na tsawon mako biyu domin bai wa ƙarin ‘yan Najeriya masu cancanta damar yin rajista kafin zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Hukumar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan kiraye-kirayen da jama’a suka yi na ƙarin lokaci saboda wasu ba su samu damar kammala rajistarsu ba kafin wa’adin farko ya ƙare.

INEC ta kuma ƙara da cewa ta samar da tsarin yin rajista ta yanar gizo ga sabbin masu rajista domin sauƙaƙa aikin da rage cunkoso a cibiyoyin rajista.

Hukumar ta buƙaci duk ‘yan Najeriya da suka kai shekara 18, da masu son canja wurin rajistarsu, gyara bayanansu ko neman sabon Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) saboda ɓacewa ko lalacewa, da su yi amfani da wannan ƙarin lokacin.

INEC ta sake jaddada aniyarta ta gudanar da sahihin zaɓe tare da ƙarfafa duk masu cancanta su kammala rajistarsu kafin sabon wa’adin ya cika.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sandan Bauchi Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Fashi da Makami A Gadau
Next Post: Gombe Ta Yi Kira Ga Jami’o’i Su Tallafa Wa Gwamnati Ta Hanyar Bincike Da Ƙirƙire-ƙirƙire

Karin Labarai Masu Alaka

Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya Afrika
Shugaba Trump Yace Akwai Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Iran Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala Afrika
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Tura Rundunar Tsaron Sham Zuwa Kakarshin Ikon Kurdawa Labarai
  • Nasarawa United Ta Kai Wasan Kusa da Ƙarshe Na Gasar Gusau/Ahlan 2026 Wasanni
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
  • Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka Amurka
  • Mayakan RSF A Sudan Suna Sace Kananan Yara A Lokacin Yake-Yaken Kasar Afrika
  • ECOWAS Ta Saka Dokar Ta Baci A Afrika Ta Yamma Afrika
  • Amurka Zata Bada Gudunwa Ga Masu Zanga-Zanga A Iran Sauran Duniya
  • Alejandro Balde Na Dab Da Komawa Manchester United Daga Barcelona Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.