Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan Sandan Bauchi Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Fashi da Makami A Gadau
Published: July 7, 2026 at 12:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da hannu a wani harin fashi da makami da fasa gida da ya faru a garin Gadau da ke ƙaramar hukumar Gamawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na safiyar ranar 8 ga Yunin 2026, lokacin da wasu mutane biyar dauke da adda da sauran makamai masu haɗari suka kutsa cikin gidan wani matashi mai shekaru 28.

A cewar rundunar, maharan sun balle ƙofar ɗakin kwanan mamacin, tare da yi masa da matarsa barazana da makamai kafin su ɗaure su, sannan suka sace babur ƙirar Jincheng, wayoyin salula na Android guda biyar, atamfofi guda goma, agogon hannu guda uku, hula ɗaya da kuɗi Naira miliyan ɗaya. An kiyasta darajar kayan da aka sace ta kai kusan Naira miliyan huɗu.

Bayan samun rahoton lamarin a ranar 3 ga Yulin 2026, jami’an ‘yan sanda sun fara bincike na sirri wanda ya kai ga kama Salisu Umar da Sadiq Shehu, dukkansu masu shekaru 20.

Sanarwar ta ce yayin gudanar da tantance waɗanda ake zargi, matar wanda aka yi wa fashin ta gano tare da nuna Sadiq Shehu a matsayin ɗaya daga cikin maharan da suka shiga ɗakinta tare da tilasta mata buɗe ƙofar gida domin sauran abokan aikinsa su shiga.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yaba wa jami’an ofishin ‘yan sanda na Gadau bisa nasarar da suka samu, tare da bayar da umarnin miƙa binciken zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin ci gaba da bincike.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar na ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere, yana mai jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Haka kuma ya buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da aikata laifuka.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Yobe Ta Sake Jaddada Ƙudirin Rage Mutuwar Yara
Next Post: Sabuwar Dama Ga Masu Zaɓe: INEC Ta Tsawaita CVR Zuwa Ƙarshen Yuli

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnonin Arewa “Mun Amince Da Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
Kungiyar Tsaro Ta NATO Tana Fuskantar Kalubale Afrika
Sojojin Amurka Sunfara Isowa Gabas Ta Tsakiya Amurka
Amurka Zata Hana Kwankwaso Shiga Kasar Amurka
Sarkin Gombe Yayin Hawan Tudun Wada Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugabannin Kiristoci Sun Halarci Filin Idi A Kaduna Domin Nuna Haɗin Kai Afrika
  • Masu Ruwa Da Tsaki 60 Sun Samu Horon Sasanta Rikici Don Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
  • Shugaba Trump Yayi Barazanar Tarwatsa Cibiyar Makamashin Iran Amurka
  • Shirin Ga Fili GA Doki Shirye-Shirye
  • Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
  • Kamaru Ta Lallasa Malawi 3-0, Ta Lashe Kofin WAFCON Na Farko A Tarihi Wasanni
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
  • Chadi Ta Sauyawa ‘Yan Gudun Hijira Matsuguni Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.