Ƙungiyar Network of Peace Journalists (NPJ) ta yaba wa Ofishin Jakadancin Jamus a Najeriya, Cibiyar Sasanta Rikicin Addinai (IMC) da Kotun Sasanta Rikici ta Jihar Kaduna (KDMDC), bisa shirya wani horo na kwanaki biyu kan Madadin Sasanta Rikici ba tare da zuwa kotu ba (ADR), wanda ya samu halartar sama da masu ruwa da tsaki 60 daga sassa daban-daban na jihar Kaduna a Najeriya.
Shugaban ƙungiyar ta NPJ, Ambassador Ibrahima Yakubu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai bayan kammala horon na kwanaki biyu.
Ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa ƙwarewar masu ruwa da tsaki wajen hana rikice-rikice, sasanta bambance-bambance da kuma inganta zaman lafiya tsakanin al’umma.
A cewarsa, horon ya haɗa sama da mahalarta 60 da suka fito daga ɓangaren shari’a, lauyoyi, ƙungiyoyin farar hula da jami’o’i, da kuma shugabannin mata da na addinai daga shiyyoyin sanatoci uku na Jihar Kaduna.
Mahalarta sun haɗa da wakilan Hukumar Korafe-Korafen Jama’a, Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Ƙasa da Ƙasa, Cibiyar Sasanta Rikicin Addinai, alkalai, lauyoyi, malamai, shugabannin mata da shugabannin addinai, da sauran masu ruwa da tsaki.
Ambassador Yakubu ya ce horon ya bai wa mahalarta damar koyon dabaru na fahimtar yanayin rikici, nazarin rikice-rikice, fahimtar nau’ikan halayen mutane da kuma hanyoyin daban-daban na Alternative Dispute Resolution (ADR).
Ya ce ilimi da ƙwarewar da mahalarta suka samu za su taimaka musu wajen shiga tsakani cikin rikice-rikicen al’umma yadda ya kamata, tare da hana ƙananan saɓani rikidewa zuwa rikici mai ɗauke da tashin hankali ko kuma shari’o’in da za su ɗauki tsawon lokaci a kotu.
Ya ƙara bayyana cewa an ƙarfafa mahalarta da su kafa abin da ya kira “tantunan sasanci” a cikin al’ummominsu da wuraren aikinsu, domin a rika magance saɓani ta hanyar tattaunawa da sasanci kafin lamarin ya kai ga shigar da ƙara a kotu.
Shugaban NPJ ya yaba wa Ofishin Jakadancin Jamus, IMC da KDMDC bisa nasarar aiwatar da shirin tare da haɗa masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Jihar Kaduna.
Ya ce shirin ya nuna muhimmancin ƙarfafa hanyoyin da al’umma ke amfani da su wajen hana rikici da kuma sasanta saɓani cikin lumana, musamman a lokacin da al’ummomi ke buƙatar samun damar tattaunawa da sasanci cikin sauƙi.
Ambassador Yakubu ya kuma yaba wa Ofishin Jakadancin Jamus da Cibiyar Sasanta Rikicin Addinai bisa ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen samar da zaman lafiya, musamman shirye-shiryen da ke ƙarfafa shigar mata cikin ayyukan samar da zaman lafiya, kare haƙƙin bil’adama da kuma ’yancin yin imani da addini.
Ya jaddada cewa saka hannun jari wajen sasanci, tattaunawa da samar da zaman lafiya mai haɗa kowa zai taimaka wajen gina al’ummomi masu ƙarfi tare da samar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya.


