Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Yara Miliyan 16 Sun Amfana Da Azithromycin A Karkashin Shirin SARMAAN
Published: September 8, 2026 at 2:59 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Yayin da manyan shugabannin harkokin kiwon lafiyar duniya ke taruwa a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu domin halartar taron duniya karo na 18 kan lafiyar jama’a, shirin SARMAAN na Najeriya na samun yabo da kulawa saboda yadda yake aiwatar da manyan shirye-shiryen inganta lafiyar yara tare da tabbatar da tsaro da kuma sa ido kan juriyar ƙwayoyin cuta ga magunguna.

An gudanar da taron ne karkashin taken “Lafiya Ba Ta Da Iyaka: Daidaito, Haɗa Kowa da Dorewa,” inda ake tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da juriyar ƙwayoyin cuta ga magunguna, daidaito wajen samun damar kiwon lafiya da kuma tsarin One Health.

A halin yanzu, shirin SARMAAN ya kai maganin Azithromycin ga sama da yara miliyan 16 a jihohi 11 na arewacin Najeriya.
Shirin ya haɗa bayar da maganin ga dimbin yara da kuma sa ido kan lafiyarsu, tare da gudanar da bincike kan juriyar ƙwayoyin cuta ga magungunan kashe ƙwayoyin cuta.

Masu gudanar da shirin sun ce wannan tsarin na tabbatar da cewa yayin da ake faɗaɗa ayyukan zuwa ga miliyoyin yara, ana kuma kiyaye matakan da suka dace na kare lafiyar jama’a.

Babban mai bincike na shirin SARMAAN kuma Daraktan Bincike a Cibiyar Nazarin Likitanci ta Najeriya, Farfesa Oliver Ezechi, ya ce bin ƙa’idojin kimiyya da kuma gudanar da manyan shirye-shiryen kiwon lafiya na iya tafiya tare.

A Najeriya, adadin mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar ya ragu daga mutuwar yara 132 cikin kowane haihuwa 1,000 a shekarar 2018, zuwa 102 cikin 1,000 a binciken Demographic and Health Survey na shekarar 2023 zuwa 2024.

Sai dai duk da wannan ci gaba, adadin ya kasance sama da burin da aka gindaya a cikin Muradun Ci Gaba Mai Ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ke nufin rage mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar zuwa 25 cikin kowane haihuwa 1,000.

Jakadiyar shirin SARMAAN, Dakta Zainab Shinkafi-Bagudu, ta ce samun daidaito na gaskiya a fannin kiwon lafiya na nufin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar cin gajiyar matakan ceton rai, ba tare da la’akari da inda yake zaune ba.

A jihar Jigawa kuma, Uwargidan Gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Umar Namadi, ta jaddada muhimmiyar rawar da iyaye mata, masu kula da yara da kuma al’umma ke takawa wajen samar da amincewa da shirin.
Ta ce haɗin kan iyaye da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da nasarar shirye-shiryen kiwon lafiyar yara.

Kwarewar shirin SARMAAN ta nuna cewa jagorancin gwamnati, amincewar al’umma da kuma hujjojin kimiyya na iya haɗuwa wajen aiwatar da manyan shirye-shiryen kiwon lafiya, tare da ba da fifiko ga tsaro da kare lafiyar jama’a.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
Next Post: Manchester United Na Cikin Manyan Kungiyoyi 10 Na Champions League

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumomin Tsaron Najeriya Ne Suka Bukaci Amurka Ta Turo Musu Sojoji Amurka
Shugaban Amurka Zai Sake Aika Jirgin Yaki Gabas Ta Tsakiya Amurka
Jirgin Sojin Saman Najeriya Yayi Hatsari a Jihar Neja Labarai
Tsohon Ma’aikacin VOA Saleh Shehu Ashaka Ya Rasu Afrika
Gwamna Bala Kauran Bauchi Ya Koma Jam’iyar APM Afrika
Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Yayi Magana Game Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Najeriya
  • Kyautata Dangantaka Tsakanin Jami’an Tsaro Da Al’umma Ce Mafita Najeriya
  • Madrid, Arsenal Da Chelsea Sun Fara Zaurancen Dan-Wasa Kenan Yildiz Wasanni
  • Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
  • Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe Afrika
  • Kwankwaso Yayi Kakkausar Lafazi Bayan Ficewar Abba Kabir Yusuf Daga NNPP Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashe Hudu Domin Inganta Kiwon Lafiya Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.