Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika
  • Yara Miliyan 16 Sun Amfana Da Azithromycin A Karkashin Shirin SARMAAN Afrika

CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
Published: September 10, 2026 at 11:35 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar “Charismatic Bishops Conference of Nigeria” (CBCN) ta bayyana goyon bayan ta ga Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.

Shugaban CBCN, Archbishop Prof. Leonard Bature Kawas, shi ne ya bayyana matsayar ƙungiyar a ranar Laraba a Birnin Abuja, a lokacin da ake gudanar da babban taron Synod na 2026 na CBCN da ICCABA a Majami’ar Kiristoci ta Ƙasa.

Kawas ya ce ƙungiyar ta yi nazari kan ayyukan gwamnatin Tinubu, tare da bayyana shirin ta na ci gaba da mara wa shugaban ƙasar baya ta hanyar addu’a, bayar da shawarwari da kuma wayar da kai.

Ya ce: “Mun goyi bayan sa a yanzu. Mun goyi bayan sa yau, za mu goyi bayan sa gobe, kuma za mu ci gaba da goya masa baya muddin yana son kasancewa shugaban ƙasar mu.”

Ya ƙara da cewa: “Wannan gida ya amince da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.”

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci shugabannin addini da su yi amfani da tasirin su wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da kyakkyawar mu’amala tsakanin al’umma gabanin zaɓen 2027.

Ya ce: “Ci gaba da haɗa kan wannan ƙasa na buƙatar fiye da matakan gwamnati. Yana buƙatar jagoranci nagari daga dukkan ɓangarorin al’umma, ciki har da jagorancin addini.”

Idris ya yi gargaɗi kan yunƙurin nuna matsalolin tsaron Nijeriya a matsayin yaƙin addini, yana mai cewa ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun kai wa ’yan Nijeriya hare-hare ba tare da la’akari da addinin su ko asalin su ba.

“Kada a bari wani zaɓe ya sa Kirista ya juya wa Musulmi baya, ko Musulmi ya juya wa Kirista baya, ko Arewa ta juya wa Kudu baya, ko wata ƙabila ta juya wa wata baya. Nijeriya tamu ce baki ɗaya,” inji shi.

Da yake wakiltar Shugaban Ƙasa Tinubu, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya yaba wa ma’abota cocin kan gudunmawar su ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, tare da kira da a samu ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin addini.

Ya ce: “Gwamnati tana buƙatar gudunmawar Kiristoci wajen kyautata ɗabi’a da tarbiyyar al’umma, yayin da Kiristoci suke buƙatar yanayin da zai ba su damar gudanar da ayyukan su da kyau. Fiye da komai, Nijeriya tana buƙatar mu yi aiki tare domin amfanin kowa.”

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
Next Post: Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19

Karin Labarai Masu Alaka

Bankin Duniya Zaibawa Kasar Mozambique Lamunin Dala Bilyan Shida Labarai
Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin Afrika
Shugaban Najeriya Tinubu Ya Amince Na Tura Jakadu Labarai
‘Yan Sanda A Tsibirin Bahamas Sun kama Mijin Wata Ba Amurkiya Amurka
Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai
ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika
  • Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita Labarai
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
  • Kwamitin Ardo Chindo Ya Buƙaci A Hana Mamaye Filayen Kiwo da Gandun Daji Afrika
  • Mataimakin Shugaban Kasa Ya Sauka A Jihar Kwara Labarai
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa Labarai
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • Gwamnatin Gombe Zata Inganta Samar Da Wuta Wajen Amfani Da Hasken Rana Kimiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.