Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin Afrika

NCCE Za Ta Ƙarfafa Koyar Da Sana’o’i A Kwalejojin Ilimi
Published: September 17, 2026 at 2:10 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ya kamata yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya sake duba tare da sauya tsarin iliminsa baki ɗaya, domin samar da waɗanda suka kammala karatu da za su iya ƙirƙirar damar aiki maimakon jira a samar musu da ayyukan yi, in ji Mataimakin Gwamnan jihar Gombe, Dakta Manassah Daniel Jatau.

Jatau ya bayyana hakane a Gombe lokacin da Sakatariyar Zartarwa na Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa (NCCE), Dakta Angela Ajala, ta jagoranci shugabannin Kwalejojin Ilimi daga jihohin Arewa maso Gabas zuwa ziyarar ban-girma ga gwamnatin jihar Gombe.

Mataimakin Gwamnan ya ce babban ƙalubalen ci gaban yankin ba wai kawai ƙara yawan matasan da ke shiga makarantu ba ne, sai dai tabbatar da cewa abin da suke koya yana haifar da ƙwarewa, kirkire-kirkire, kasuwanci, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a.

Ya ce ƙara samun wahalar da waɗanda suka kammala karatu ke fuskanta wajen samun ayyukan yi a hukumance ya fara rage sha’awar neman ilimi a wasu al’ummomi. Saboda haka, ya ce akwai buƙatar sake fahimtar ilimi a matsayin wata hanya ta inganta rayuwa a kusan kowace sana’a ta halal.

Ya ce, “Manomi, ɗan sana’a, ɗan kasuwa ko ƙwararren ma’aikaci mai ilimi ya kamata ya iya amfani da ilimi da kirkire-kirkire wajen inganta aikinsa da kuma samar da ƙarin daraja.”

A cewar Jatau, wannan sauyi na da muhimmanci musamman ga yankin da ke da dimbin matasa, domin a mayar da su wata babbar kadara ta tattalin arziki.

Saboda haka, ya yaba da matakin NCCE na shigar da koyar da sana’o’i da ƙwarewar aiki cikin tsarin koyar da malamai, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da malamai waɗanda ke da takardun ilimi tare da ƙwarewar aiki.

Mataimakin Gwamnan ya kuma ƙalubalanci malamai da su ƙara ɗaukar alhakin kare martabar aikin koyarwa, yana mai cewa yadda jama’a za su kalli aikin koyarwa zai dogara matuka da jajircewa, ɗabi’a da kuma kwarewar malamai.

Ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, Kwalejojin Ilimi, al’ummomi da sauran masu ruwa da tsaki domin tunkarar ƙalubalen da ke fuskantar ilimi a yankin.

Jatau ya kuma ja hankalin jama’a kan barazanar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa, yana mai gargadin cewa zuba jari a fannin ilimi na iya samun ƙarancin tasiri idan a lokaci guda matasa na fuskantar matsalar shaye-shaye da sauran munanan ɗabi’u.

NCCE TA BAYYANA SABON TSARIN HORAR DA MALAMAI

Tun da farko, Sakataren Zartarwa na NCCE, Dakta Angela Ajala, ta gabatar da hangen nesa kan sauye-sauyen da ake shirin aiwatarwa a fannin horar da malamai, inda ta bayyana Kwalejojin Ilimi a matsayin cibiyoyin da ke da muhimmiyar rawa wajen samar da ƙwararrun ma’aikata masu iya dacewa da sauyin zamani.

Ta ce malamai su ne ginshiƙin ci gaban ƙasa, domin ingancin kowace sana’a ko fanni na aiki yana da alaƙa da ingancin mutanen da suka horar da kuma koyar da waɗanda ke cikinsa.

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin sabon tsarin shi ne Dual Mandate, wato tsarin da zai bai wa Kwalejojin Ilimi damar bayar da takardar National Certificate in Education (NCE) tare da shirye-shiryen digiri.

Ajala ta bayyana cewa ƙarƙashin sabon tsarin na shekaru biyar, ɗalibai za su samu damar samun NCE, Bachelor of Education (B.Ed.), da kuma takardar shaidar ƙwarewar sana’a da ake amincewa da ita a duniya.

Ta ce manufar ita ce samar da malamai waɗanda ba kawai suka ƙware a fannin koyarwa ba, har ma suke da kyawawan ɗabi’u da kuma ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da ƙarfin tattalin arzikinsu.

Ajala ta kuma bayyana cewa ana sa ran kowace Kwalejin Ilimi za ta kafa cibiyar koyar da sana’o’i da ƙwarewa, wadda za ta kasance a buɗe ga ɗalibai da kuma matasan da ke makwabtaka da cibiyar.

Ta ce cibiyoyin za su samar da damar koyon sana’o’i da samun takardun shaidar ƙwarewa a matakai daban-daban, ta yadda matasa za su samu ƙwarewar da za su iya amfani da ita a Najeriya da sauran ƙasashe.

Ga yankin Arewa maso Gabas, inda samar da ayyukan yi da bai wa matasa damar dogaro da kansu ke daga cikin manyan ƙalubalen ci gaba, wannan shiri na iya bai wa Kwalejojin Ilimi wata sabuwar rawa wadda ta wuce horar da malamai kawai zuwa samar da ƙwarewa ga al’ummomin da suke kewaye da su.

Sakataren Zartarwar NCCE ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da su mayar da manufofin Dual Mandate cikin dokokin jihohinsu ta hanyar Majalisun Dokokin Jihohi, tana mai cewa samar da ingantaccen tsarin doka zai bai wa Kwalejojin Ilimi na jihohi da masu zaman kansu damar shiga shirin yadda ya kamata.

Ta kuma yi kira da a ƙara zuba jari da samar da tallafin musamman ga cibiyoyin, tana mai cewa Kwalejojin Ilimi ba za su iya magance dukkan ƙalubalen da ke fuskantar fannin horar da malamai su kaɗai ba.

Ajala ta kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, masana’antu, ƙungiyoyin ci gaba, hukumomin da ke da alhakin tsara dokoki da sauran masu ruwa da tsaki, domin inganta gine-gine, ƙwarewar ma’aikata da damar koyon sana’o’i a yankin.

Taron ya mayar da hankali kan batutuwa biyu masu alaƙa da juna a fannin ilimi a Arewa maso Gabas: ingancin malaman da ake samarwa da kuma yadda cibiyoyin ilimi za su iya bai wa matasa ƙwarewar da ta dace da sauyin tattalin arziki.

Haka kuma, ziyarar ta ba da damar jaddada wasu daga cikin abubuwan da Gwamnatin Jihar Gombe ke bai wa muhimmanci a fannin ci gaba.

A matsayin karramawa ga gudunmawar gwamnatin jihar wajen ilimi da ci gaba, an bai wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, Dan Majen Gombe, lambar yabo ta ƙwarewa.

Haka kuma, an bai wa Dakta Angela Ajala kwafin Gombe State Development Agenda (DEVAGOM) da kuma Gombe State Government Scorecard, domin ba wa shugabannin NCCE damar fahimtar abubuwan da jihar ta sa a gaba da kuma nasarorin da gwamnatin ta ce ta samu.

Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi; Kwamishiniyar Ilimi, Farfesa Aishatu Umar Maigari; sauran Kwamishinoni da manyan jami’an gwamnati; masu kula da harkokin ilimi; malamai da jami’an jami’o’i da kwalejoji; ’yan jarida; da kuma Provosts na Kwalejojin Ilimi daga sassan Arewa maso Gabas.

Mahalarta taron, waɗanda Shugaban Federal College of Education (Technical), Gombe, Dakta Muhammad Ghazali Abdul Hamid, ya jagoranta, sun haɗa da shugabannin Kwalejojin Ilimi na tarayya, jihohi da masu zaman kansu daga jihohin Gombe, Bauchi, Borno, Taraba, Adamawa da Yobe.

Saƙon da ya fito daga taron shi ne cewa, a mataki na gaba na bunƙasa ilimi a Arewa maso Gabas, akwai buƙatar a wuce matakin samar da takardun shaida kawai, zuwa gina ilimi, ƙwarewa, kirkire-kirkire da kuma damar samar da abubuwan da za su taimaka wajen sauya tattalin arziki da rayuwar al’ummar yankin na dogon lokaci.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Rundunar ’Yan Sandan Gombe Ta Raba Makuden Kudade Ga Iyalan Jami’an Da Suka Rasu
Next Post: Mutane 13 Sun Rasa Rayukansu A Sabon Harin Boko Haram A Madegwa

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumomin Kasar China Suna Goyon Bayan Somaliya Labarai
Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai
Sarkin Gombe Yayin Hawan Tudun Wada Labarai
Kamfanin Jiragen Saman Ethiopia Zai Kafa Babban Filin Jirgi Afrika
Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran Amurka
  • Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika
  • Farashin Mai Ya Doshi Dala 100 Kowacce Ganga Afrika
  • Makokin Ashura: An Gudanar Da Taron Tunawa Da Aliyul Asghar A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutu Najeriya
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • FIFA, Ta Tabbatar Da Ranar Mika Sunayen ‘Yan Wasa AFCON 2025. Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.