Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini Afrika
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika

Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji
Published: September 15, 2026 at 9:29 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Kebbi a arewacin Najeriya ta ƙaryata rahoton da ya ce ta sayi kujerun Hajji har na Naira biliyan 21.5 domin taɓawa ga ƴan jihar.

Hajj Reporters ta rawaito cewa wani mai suna Evangelist Ibrahim Dikko ne ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗe don rabawa mutane kujerun aikin Hajji.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan jihar, Ahmed Idris ta fitar, gwamnatin ta ce sam wannan rahoto ƙarya ne domin kuɗin da ake magana akai, na kujeru ne da maniyyata su ka biya.

“An ja hankalinmu kan wani labari da Evangelist Ibrahim Dikko ya wallafa, inda ya yi zargin cewa Gwamnatin Jihar Kebbi ta ware sama da Naira biliyan 21.5 domin daukar nauyin alhazan jihar zuwa Ƙasa Mai Tsarki.

“Muna son bayyana wa a fili cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne, kuma ya ƙunshi bayanan da za su iya yaudarar jama’a da kuma rashin sahihanci.

” Domin magance duk wata shakka, Gwamnatin Jihar Kebbi ba ta ware Naira biliyan 21.5, ko wani adadin kuɗi, domin ɗaukar nauyin aikin Hajjin 2027 ba.

” Kuɗaɗen da aka ambata a cikin labarin, kuɗaɗe ne da kowane maniyyaci zuwa aikin ya biya domin biyan kujerar Hajji.

“Naira biliyan 21.5 da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi ta tura, na wakiltar kuɗaɗen da sama da maniyyata 3,000 da ke shirin zuwa aikin Hajjin 2027 suka biya,” in ji Idris.

Ya kara da cewa hukumar na aiki ne a matsayin hanyar da ake bi wajen karɓa, sarrafawa da kuma tura kuɗaɗen da maniyyata su ka biya zuwa Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Najeriya (NAHCON).

Ya ƙara da cewa ba a yi amfani da kuɗaɗen gwamnati ko wani kaso daga cikin kasafin kuɗin jihar wajen biyan waɗannan kuɗaɗen Hajji na kowane mutum ba.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
Next Post: Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini

Karin Labarai Masu Alaka

Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe Afrika
Mayakan Boko Haram Da ISWAP Sun Kai Hari Cikin Dare Afrika
Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya Labarai
Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini
  • Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugabannin Kasashen Sahel Sunyi Taro a Mali Afrika
  • Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi Afrika
  • Kasar Iran Zata Kai Hare Haren Ramuwar Gayya Isra’ila Afrika
  • NDLEA Ta Fara Binciken Kwakwaf Akan Wasu ‘Yan Mata Dake Kai Kwaya Gidan Yari Labarai
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika
  • Yan Najeriya na ci gaba da maida martani akan sabuwar dokar zabe da majalisar Dattawan kasar ta Amince dashi Najeriya
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Yayin Rikici A Uganda Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.