Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Gombe @ 30, Najeriya @ 66: Inuwa Yace Jihar Za Ta Kara Zama Cibiyar Tattalin Arziki A Arewa
Published: October 1, 2026 at 7:29 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya sake jaddada kudirinsa na kara habaka ci gaban jihar, fadada damar tattalin arziki da kuma karfafa nasarorin da aka samu a muhimman bangarori, yayin da jihar ke bikin cika shekaru 30 da kafuwa tare da bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Najeriya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na musamman na bikin ranar 1 ga Oktoba, 2026, inda ya ce bikin cikar jihar shekaru 30 da kuma ranar samun ‘yancin kan Najeriya, wata dama ce ta duba irin sauye-sauyen da Gombe ta samu cikin shekaru uku da suka gabata, tare da tsara sabuwar hanyar da za ta bi wajen samun karin ci gaba.

Ya ce tun bayan kirkirar jihar a ranar 1 ga Oktoba, 1996, Gombe ta sauya daga sabuwar jiha zuwa wata muhimmiyar cibiyar tattalin arziki da gudanar da harkokin mulki a yankin Arewa maso Gabas, sakamakon tsare-tsaren raya kasa, zuba jari a ababen more rayuwa da sauye-sauyen da ake aiwatarwa domin samar da yanayi mai kyau ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.

Gwamnan ya danganta tafiyar ci gaban jihar da Tsarin Raya Gombe na Shekaru 10, DEVAGOM, wanda ya ce yana samar da dogon tsarin da zai tabbatar da samun ci gaba mai dorewa da kuma shigar kowa cikin harkokin raya jihar.

A cewarsa, an tsara DEVAGOM ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, kuma yana jagorantar ayyukan gwamnati da zuba jari a muhimman bangarori da suka hada da bunkasa ilimin dan Adam, ababen more rayuwa, habaka tattalin arziki, kare muhalli da inganta rayuwar al’umma.

Gwamna Inuwa ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da shirye-shirye a bangarorin ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi, noma, masana’antu, kare muhalli, sauye-sauyen ma’aikatar gwamnati, saukaka harkokin kasuwanci da kuma tallafawa matasa da mata.

A bangaren ilimi, ya ce gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta gine-ginen makarantu da karfafa bangaren ma’aikata ta hanyar ginawa, gyarawa da bunkasa makarantu tare da daukar kwararrun malamai domin rage karancin ma’aikata da inganta koyarwa da koyo.

A fannin kiwon lafiya kuwa, gwamnati ta zuba jari wajen farfado da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 228, da inganta asibitocin gwamnati da kuma kara karfin ayyukan kiwon lafiya na kwararru.

Ya kara da cewa an dauki karin ma’aikatan lafiya, an inganta tsarin albashinsu, sannan aka fadada tsarin inshorar lafiya domin kara yawan al’ummar da za su samu kulawar lafiya mai sauki.

Game da hanyoyi, Gwamnan ya ce jihar ta samu gina da gyaran fiye da kilomita 1,000 na hanyoyi karkashin shirin Network 11-100 da sauran ayyuka.

A cewarsa, ayyukan sun taimaka wajen inganta zirga-zirga tsakanin al’ummomi, bude yankunan karkara da kuma saukaka safarar amfanin gona, mutane da kayayyaki.

Ya kuma ce ci gaban Three-Arms Zone da sauran ayyukan raya birane sun taimaka wajen sauya fasalin babban birnin jihar Gombe.

A fannin masana’antu da jawo masu zuba jari, Gwamnan ya ce gwamnatinsa na ci gaba da bunkasa Muhammadu Buhari Industrial Park, mai fadin hekta 1,000, wanda aka tsara shi a matsayin babbar cibiyar masana’antu da zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu.

Ya ce hakan na tafiya tare da kokarin saukaka harkokin kasuwanci da samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari da kuma samar da ayyukan yi.

A bangaren noma da kiwo, Gwamnan ya ce gwamnati na mayar da hankali wajen kara karfin samar da amfanin gona da kiwo ta hanyar Agro-Livestock Development Zone, da nufin tallafawa manoma da masu kiwo, bunkasa sarrafa amfanin gona da kuma karfafa gudunmawar bangaren wajen samar da abinci da habaka tattalin arziki.

Game da kare muhalli kuwa, ya ce gwamnati ta kara kaimi wajen dakile matsalar kwararowar kasa da zaizayar kasa ta hanyar ayyukan dakile zaizayar kasa da farfado da muhalli.

Ya ce shirin Gombe Goes Green (3G) na kuma taimakawa wajen dasa itatuwa da farfado da muhalli domin dakile hamadar da kuma tinkarar kalubalen sauyin yanayi.

A bangaren sauye-sauyen ma’aikatar gwamnati da jin dadin ma’aikata, Gwamna Inuwa ya ce gwamnatinsa ta ci gaba da biyan albashi a kan lokaci tare da kokarin magance basussukan da ta gada.

Ya bayyana biyan bashin kudaden garatuti da aka gada daga tsoffin ma’aikatan gwamnati a matsayin daya daga cikin muhimman nasarorin da aka samu.

Gwamnan ya ce gwamnati ta kuma aiwatar da shirye-shiryen tallafawa matasa da mata da suka hada da koyar da sana’o’i, bunkasa kasuwanci, noma da samar da damar shiga harkokin tattalin arziki.

Ya ce dukkan wadannan matakai na daga cikin kokarin gwamnatinsa na mayar da manufofin DEVAGOM zuwa ayyukan da jama’a za su iya gani da kuma amfani da su, tare da kara bunkasa nasarorin da aka samu.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce: “Yayin da muke bikin wadannan muhimman tarihi, muna sane da cewa tafiyar da ke gabanmu na bukatar karin jajircewa. Don haka, muna sake tabbatar da kudirinmu na gina kan nasarorin shekaru 30 da suka gabata, karfafa zaman lafiya da hadin kai, bunkasa tattalin arziki mai bai daya, fadada damar jama’a da kuma sanya Gombe a kan turbar ci gaba mai dorewa.”

A matsayinsa na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya ya taya Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, da daukacin ‘yan Najeriya murnar cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai.

Ya bayyana tafiyar Najeriya tun bayan samun ‘yancin kai a matsayin tafiya mai cike da juriya, bambancin al’adu, kalubale da kuma ci gaba.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen kare hadin kai, zaman lafiya, adalci da dimokuradiyya, yana mai cewa bambancin da ke tsakanin al’ummar kasar wata hanya ce ta karfafa kasa.

Ya ce: “Duk da kalubalen da muka fuskanta a wannan tafiya, har yanzu muna da cikakken imani da Najeriya. Dole ne mu ci gaba da karfafa hadin kanmu, zurfafa dimokuradiyyarmu, inganta zaman lafiya da adalci, tare da yin aiki tare domin gina kasa da ta dace da sadaukarwa da burin wadanda suka gabace mu.”

Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar Gombe da ‘yan Najeriya da ke cikin gida da kasashen waje da su yi amfani da wadannan bukukuwa biyu wajen sabunta kudurinsu na gina kasa da kuma tabbatar da ci gaba na bai daya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Bayan Sake Zaben Fidda Gwani PDP Ta Dakatar Da Mailantarki Da Garry
Next Post: Najeriya @ 66: Tinubu Ya Ce Gwamnati Za Ta Kara Zuba Jari A Noma, Masana’antu Da Bunƙasa Matasa

Karin Labarai Masu Alaka

Turkiyya Ta Zargi Alakar Isra’ila Da Somaliya Afrika
Kamfanin Jiragen Saman Ethiopia Zai Kafa Babban Filin Jirgi Afrika
Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe Afrika
Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya Afrika
Lakurawa Sun Kashe A Ƙalla A Mutane 34 A Jihar Kebbi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • Tabbas Atiku Abubakar Ya Karbi Katin Jam’iyyar ADC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia Afrika
  • Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NITDA Da GOSIDEC Sun Horar Da Ma’aikatan Gombe Don Inganta Ayyukan Gwamnati Afrika
  • Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai Afrika
  • Shugaba Putin Ya Bukaci Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.