Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Hukumar NEDC Ta Ƙaddamar Da Shirin Inganta Sufuri
Published: October 12, 2026 at 3:06 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya (NEDC) ta ce tana shirin samar da kekunan adai-daita sahu masu amfani da wutar lantarki guda 10,000, motocin haya masu amfani da wutar lantarki guda 300, da manyan motocin bas masu amfani da wutar lantarki guda 30 domin inganta sufuri da samar da ayyukan yi a yankin.

Mai kula da ayyukan hukumar ta NEDC, Mohammed Alkali, ne ya bayyana hakan a wani taron wayar da kan masu ruwa da tsaki kan sufuri mai amfani da wutar lantarki da aka gudanar a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Taken taron shi ne, “Samar da Makamashi a Arewa maso Gabas: Rungumar Sufuri Mai Amfani da Wutar Lantarki Domin Samar da Muhalli Mai Tsabta, Ingantaccen Tsari da Wadata.”

Shi ma da yake jawabi, Babban Daraktan Kamfanin Attahir Enterprises, Bunu Abatcha, ya ce sufuri mai amfani da wutar lantarki na da damar taimakawa wajen magance matsalolin sufuri da samar da sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga a yankin.

Abatcha ya jaddada buƙatar samar da tsari mai ɗorewa da zai tabbatar da kula da motocin yadda ya kamata, samar da kuɗaɗen gudanarwa da kuma bai wa masu ruwa da tsaki damar cin moriyar shirin na dogon lokaci.

Ya ce shirin ya yi daidai da ajandar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta Renewed Hope da kuma Babban Tsarin Samar da Zaman Lafiya da Ci Gaban Arewa maso Gabas, wanda ya bayyana sufuri a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen bunƙasa yankin.

Abatcha ya kuma yi kira da a ƙara sa hannun kamfanoni masu zaman kansu wajen samar da kuɗaɗen gudanarwa, tafiyar da harkokin motocin da kuma kula da su, yana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori daban-daban shi ne mabuɗin nasarar shirin.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: NAWOJ Ta Yi Kira Ga Gwamnati Da Iyaye Kan Illolin Auren Wuri
Next Post: An Sanya Hannu kan Yarjejeniyar Ci Gaba Tsakanin Kamfanin Ashaka Da Maiganga

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Ya Kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Afrika
Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki Labarai
Haryanzu Abubakar Malami Da Dansa Suna Hannun Hukumar EFCC Labarai
Wata Mace Ta Mutu A Hannun ‘Yan-Fashin Daji, Wata Ta Haihu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Maryam Dan’azumi Ta Zama Abin Alfahari Ga Najeriya Bayan Lashe Gasar Alƙur’ani Ta Duniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rasha Ta Nuna Kudurin Cimma Zaman Lafiya Da Ukraine Amurka
  • Wani Abu Ya Fashe A Asibitin Bagudo Dake Jihar Kebbi Tsaro
  • Jirgin Hakar Mai Daga Turkiyya Ya Isa Mugadishu Afrika
  • Jam’iyar APC A Jihar Gombe Ta Tsayar Da Jamilu Isiyaku Gwamna Takarar Gwamna Afrika
  • Shugaban Kasar Iran Yace Kasar Bata Da Kiyayya Tsakaninta Da Amurkawa Afrika
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
  • An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.