Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen 2027, inda ya naɗa tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, a matsayin Darakta Janar na kwamitin.
A cewar sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Asabar, Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, zai kasance Sakataren kwamitin.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai jagoranci kwamitin a matsayin Shugaba, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai kasance Mataimakin Shugaba na Farko.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, zai kasance Mataimakin Shugaba na Biyu, yayin da Sakataren Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru, zai zama Mataimakin Sakataren kwamitin. Hadiza Bala-Usman kuma za ta kasance Mataimakiyar Sakatariya.
Kwamitin zai kuma samu tawagar manyan masu ba da shawara, ciki har da tsohon Shugaban APC, Bisi Akande; fitaccen ɗan jarida kuma ɗan siyasa, Segun Osoba; tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha; tsohon Shugaban APC, Abdullahi Adamu; da Sanata Florence Ita-Giwa.


