Al’ummar unguwar Libiya da ke cikin birnin Gombe sun bi sahun sauran al’ummomin duniya wajen bikin Ranar Abinci ta Duniya, inda aka shirya taron a gidan dagacin unguwar, Malam Isah Muhammad Malam Sidi.
Da take jawabi a wajen taron, Kwamishiniyar Women Community in Africa (WCA), Mrs. Ruth Abner, wadda mataimakiyarta, Mrs. Rahab Maina Lah, ta wakilta, ta taya al’ummar Libiya murnar zagayowar wannan rana.
Ta nuna godiya ga ƙungiyoyin jin ƙai da sauran abokan hulɗa bisa gudummawar da suke bayarwa, inda ta bayyana cewa duk da ba ta samu halartar taron da kanta ba, tana tare da al’ummar da zuciyarta.
Mrs. Abner ta bayyana cewa ci gaban al’umma ba aikin mutum ɗaya ba ne, sai dai yana buƙatar haɗin kai tsakanin ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki.
Saboda haka, ta yi kira ga WCA, Voice of Women, Adamu Yola Foundation da shugabannin matan Libiya da su ci gaba da haɗa kai wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.
Ta kuma buƙaci mahalarta taron da su mai da hankali ga horon da ake ba su, domin su iya isar da ilimin da suka samu ga sauran waɗanda ba su samu damar halartar taron ba.

Kwamishiniyar ta ce taken bikin na wannan shekara shi ne, “Mu samar da abubuwan da za su ciyar da mu gobe tun daga yau, domin abinci yana taimaka mana girma. Idan muka haɗa kai, babu yunwa da ƙuncin rayuwa a cikin al’ummarmu.”
Ta kammala jawabin nata da godiya ga dukkan waɗanda suka bayar da gudummawa wajen ganin an gudanar da bikin cikin nasara.
A nasu ɓangaren, Ikilima Abdulkareem Fatima, wadda ita ce shugabar kamfanin Ekfat Global Nigeria Limited, da Dr. Leah Iliya Jalo, mai kula da tallafi da haɗin gwiwa a WCA, sun horas da matan kan hanyoyin sarrafa masara, shinkafa, wake da gero zuwa nau’o’in abinci masu gina jiki.
Sun bayyana muhimmancin shirya abinci mai ƙara ƙoshin lafiya da inganta jini, domin kare lafiyar iyalai da kuma rage haɗarin kamuwa da cututtuka, musamman a wannan lokacin sanyi da ake kira harmattan.
Haka kuma, sun koyar da matan hanyoyin zamani na noman dankali da kayan lambu a gida, domin taimaka musu wajen samar da abinci mai inganci da inganta rayuwar iyalansu.
A nasa jawabin, mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Barr. Bulus Maori, ya yi magana kan muhimmancin zaman lafiya da zaman tare a cikin al’umma, inda ya bayyana shi a matsayin ginshiƙin ci gaba.
A cewarsa, idan babu zaman lafiya, hatta rayuwar iyali za ta shiga cikin wahala, kuma babu wata al’umma da za ta samu ci gaba ba tare da zaman lafiya ba.
Ya ƙara da cewa zaman lafiya yana ƙarfafa haƙuri da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Saboda haka, ya buƙaci jama’a da su guji ƙabilanci da son kai, tare da rungumar haɗin kai da fahimtar juna domin samun nasara a rayuwa.
Da take gabatar da saƙon godiya a madadin matan Libiya, ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da horon, Binanina Bahaushe, ta bayyana godiyarta ga WCA bisa koya musu dabarun girke-girke da sarrafa abinci.
Ta yi alƙawarin cewa za su yi amfani da ilimin da suka samu a rayuwarsu ta yau da kullum, tare da yaɗa shi ga sauran matan da ba su samu damar halartar horon ba.
Binanina ta bayyana horon a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma zai taimaka wajen kare lafiya da inganta rayuwar iyalai.
A nasa jawabin, dagacin unguwar Libiya, Malam Isah Muhammad Malam Sidi, ya gode wa ƙungiyar WCA bisa zaɓar al’ummarsa domin gudanar da bikin.
A madadin daukacin al’ummar unguwar, ya nuna matuƙar godiyarsa ga masu shirya taron da dukkan baƙi, tare da yi musu addu’ar Allah Ya mayar da su gidajensu lafiya.Taron ya mayar da hankali ne kan wayar da kai game da muhimmancin abinci mai gina jiki, ƙarfafa dabarun sarrafa abinci a gida, inganta noman kayan lambu da kuma bunƙasa zaman lafiya domin samun ci gaba mai ɗorewa a cikin al’umma.


