Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya, hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da gudanar da bincike tare da hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen cin zarafin ‘yan jarida a kasar.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da Shugabanta na Kasar, Alhassan Yahya, ya fitar domin tunawa da Ranar Yaki da Rashin Hukunta Masu Laifukan da ke Kai Hare-Hare kan ‘Yan Jarida ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 2 ga watan Nuwamba na kowace shekara.
NUJ ta sake jaddada kudirinta na kare ‘yancin aikin jarida, kare rayuka da mutuncin ma’aikatan kafafen yada labarai, tare da tabbatar da an yi adalci ga dukkan ‘yan jaridun da ake tsoratarwa, muzgunawa, tsarewa ba bisa ka’ida ba ko kuma kai wa hari yayin gudanar da ayyukansu.
Sanarwar ta bayyana cewa aikin jarida shi ne ginshikin dimokuradiyya mai inganci, saboda yana taimakawa wajen sanya masu rike da madafun iko a bisa ka’ida, ba wa al’ummomin da ba su da karfi damar bayyana matsalolinsu, da kuma tabbatar da hakkin jama’a na samun sahihan bayanai.
Kungiyar ta kuma bukaci jami’an tsaro da hukumomin gwamnati su rika kallon ‘yan jarida a matsayin muhimman abokan tafiyar da dimokuradiyya, maimakon daukarsu a matsayin abokan gaba.
Bugu da kari, NUJ ta bukaci hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin kafafen yada labarai, kungiyoyin fararen hula da abokan huldar kasa da kasa domin samar da ingantattun matakan tsaro da hanyoyin agajin gaggawa ga ‘yan jaridun da ke aiki a wuraren da ke da hadari.
Kungiyar ta jaddada cewa barazana ga wani dan jarida a ko’ina, barazana ce ga dimokuradiyya a duk duniya, don haka ta yi kira ga kungiyoyin kare hakkin bil’adama da sauran al’umma da su hada kai wajen neman samar da yanayin da ‘yan jarida za su gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.
A karshe, NUJ ta bayyana cewa babu wani dan jarida da ya kamata ya rasa tsaro, ‘yanci ko rayuwarsa saboda gudanar da aikin bayar da rahoton gaskiya.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Shugaban NUJ na Kasa, Alhassan Yahya, ta fito ne daga Sakatariyar Kungiyar ta Kasa da ke Abuja.


