Amurka da Isra’ila sun kai hari kan Iran yau Asabar, inda suka auna manyan shugabannnin kasar, suna masu kiran da a kifar da gwamnatin kasar, ita kuma Iran ta maida martani tare da harba makamai masu linzami kan Isra’ila da kasashe makwabta.
Shugaba Donald Trump, a mataki da ake kallo a zaman kasada mafi girma a manufofin harkokin wajen gwamnatinsa, ya kaddamarda yaki kan kasar da Amurka take kallo a zaman makiyarta na shekaru masu yawan gaske, yace harin ta kai shine da nufin kawar da barazana, da kuma tabbatar da ganin Iran bata habaka makaman Nukiliya ba.
Yayi kira ga jami’an tsaron kasar su ajiye makaman su, daga nan ya gayyaci al’umar kasar su kifar da gwamnatin kasar da zarar an kawo karshen hare hare da ake kaiwa kan kasar.
Tehran ta kira harin da aka fara da safiyar ranar asabar kuma ya auna sassa daban daban na kasar, da cewa hari da aka kai mata ba tare da takala ba, kuma baya bisa doka.
Tashar talabijin ta kasar da ake kira -Al-Alam, tace shugaban addinin kasar Ali Khameni, wadda ba’a ji daga gareshi ba zuwa yanzu, zai yi jawabi nan ba da jumawa ba.
A birane a duk fadin kasar, karar fashe fashe sun janyo tsoro. Mazauna biranen suna gaggawar kwaso yara daga Makaranta, da gudu daga wurare da suke zaton za’a kai wa hari.
Isra’ila ta hana jama’a yin tarurruka, ta rufe makarantu da masana’antu, kuma ta kawashe maras lafiya a asibitoci zuwa wurare dake karkashin kasa, a dai dai lokacin da Iran ta harba makamai masu linzami da ta auna kan Isra’ila, a zaman martanin harin da Amurka da Isra’ila suka kai mata.
Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ayyana dokar ta baci a duk fadin kasar, ya gargadi jama’a dangane da hare hare da Iran zata kai mata da makamai masu linzami da jirage da basu da matuka.


