Amurka da wasu gaggan kasashe, cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da suka bayar ranar Alhamis sun bayyana matukar takaicin ganin “ana ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta, har dana baya bayan nan, a gabashin jamhuriyar demokuradiyyar Kwango, daga nan suka yi kira ga dukkan sassa da rikicin ya shafa su sake kudurin kawo karshen fada da suke yi su koma kan teburin shawarwari.
Amurka Da Tarayyar Turai Sun Fidda Sanarwa


