Shugaban Amurka Donald ranar a laraba ya bayyana cewa Amurka ta kama wani jirgin dakon mai dake da takunkumi a kansa, a dab da gabar ruwan kasar Venezuela, matakin da ya janyo tashin farashin mai a kasuwannin duniya tare da kara wutar tankiya a tsakanin Amurka da Venezuela.
Wannan lamarin shine na farko a kan wani jirgin dakon man fetur da aka samu tun lokacin da Trump ya bada umurnin girke sojoji da makamai masu yawa a yankin.
Amurka tana kai hare-hare a kan kananan jiragen ruwan da tayi zargin cewa na safarar muggan kwayoyi ne, abinda ya sa ‘yan majalisa da kwararru a fannin shari’a suke nuna damuwa.
Antoni janar ta tarayyar Amurka, Pam Bondi, ta wallafa a shafin X cewa hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayyar Amurka, da hukumar tsaron cikin gida ta Amurka, da dogarawan gabar teku tare da tallafin sojoji sun aiwatar da takardar iznin kama wani jirgin ruwan dakon danyen mai da ake amfani da shi wajen jigilar man fetur da aka kafa ma takunkumi daga Venezuela da Iran.
Wani bidiyo na kasa da minti daya da Bondi ta wallafa ya nuna wasu jiragen helkwafta biyu sun doshi wani jirgin ruwa, inda aka ga dakaru dauke da makamai suna sauka ta igiyoyi a kan jirgin ruwan.
Jami’an gwamnatin Trump ba su fadi sunan wannan jirgin ruwan dakon mai ba, amma wani kamfanin sarrafa harkokin zirga zirgar jiragen ruwa na Britaniya mai suna Vanguard yace an kama jirgin ruwa mai suna Skipper a ranar laraba a gabar Venezuela.
Amurka ta sanya takunkumi acan baya a kan wannan jirgi, lokacin ana Kiransa da sunan Adisa, a saboda abinda amurka ta kira hannu dumudumu wajen safarar man kasar Iran.
Jirgin ruwan ya baro babbar tashar lodin mai ta kasar Venezuela a Jose tsakanin 4 da 5 ga watan nan na Disamba, a bayan da yayi lodin ganga miliyan daya da dubu dari daya na man Venezuela.
Farashin mai ya tashi a kasuwannin duniya a bayan da aka samu labarin kama wannan jirgin ruwa.


