Hambarraren shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana a gaban wata babbar kotu ta kasar Amurka da ke unguwar Manhattan a birnin New York ranar Litinin don fuskantar tuhumur da Amurka ta ke masa na safarar miyagun kwayoyi, bayan da cafkoshi da Donald Trump ya yi ya bada mamaki, ya kuma karkada zukatan shugabannin duniya, ya kuma bar hukumomi a Caracas, babban birnin Venezuela da tunanin yadda zasu bullowa abun.
Ana sa ran Maduro zai amshi laifin sa ko akasin hakan a yayin da ya je gaban alkalin gunduma na kasa Alvin Hellerstein, kuma an daure hannayen Maduro, yayin da aka taho da su da Jami’an tsaro daga wani gidan kaso a Brooklyn da safiyar ranar litinin zuwa wani jirgi me saukar ungulu, wanda zai kai su kotun da ke Manhattan.
Ana cikin Wannan dambarwa, shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterrres ya nuna damuwar sa game da rashin kwanciyar hankali a Venezuela, da kuma dacewar abun da Trump ya yi a hukunce, wanda ya kasance mamaya mafi daukan hankali da kasar Amurka ta taba kaiwa kasashen kudancin yankin Amurka tun shekarar 1989 da ta kai mamaya kasar Panama.


