Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta ce dakarun sojojinta sun murkushe wani yunkurin juyin mulki, a bayan da wasu sojoji suka fito cikin tashar telebijin ta ƙasar suna iƙirarin kwace mulki.
Wannan yunkurin juyin mulki na baya bayan nan a yankin Afirka ta Yamma, inda sojoji suka kwace mulki a makwabtan Benin, watau Nijar da Burkina Faso, da kuma a ƙasashen Mali da Guinea-Conakry.
Ko a watan da ya shige ma, sojojin sun kwace mulki a kasar Guinea-Bissau.
Da sanyin safiyar yau lahadi, sojoji akalla 8 suka fito a gidan telebijin na kasar, wasu ɗauke da bindigogi, su na sanar da cewa wani kwamitin soja a karkashin jagorancin Kanar Tigri Pascal, ta karɓe ragamar mulkin ƙasar, tare da dakatar da yin aiki da tsarin mulki da kuma rufe bakin iyakokinta ta sama da kasa da ta ruwa.
‘Yan sa’o’i kaɗan a bayan wannan, ministan harkokin cikin gidan Benin, Alassane Seidou, ya fito a telebijin na ƙasa yana fadin cewa rundunar sojoji ta murkushe juyin mulkin.
Seidou yayi kira ga jama’a da su fito su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Wani kakakin gwamnatin Jamhuriyar Benin, yace ya zuwa yammacin nan agogon kasar, an kama mutane akalla 14 dangane da yunkurin juyin mulkin.


