An tura rundunar dakarun tsaron kasar Sham zuwa birnin dake karkashin ikon sojojin ‘yan tawayen Kurdawa a arewa maso gabashin kasar. Wannan na daga cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ke goyon baya na ganin an hade yankunan da Kurdawan ke da iko akai tare da fadar gwamnatin Damascus domin kasancewa karkashin gwamnati daya.
Yarjejeniyar ta tsagaita ci gaba da gwabza fada tsakanin gwamnatin shugaba Ahmed al-Sharaa da dakarun ‘yan tawayen Kurdawa na SDF, wadanda yankunan da suke da madafun iko a kai a gabas da arewacin kasar yanzu suka dawo karkashin ikon gwamnati.
Tsarin wanzar da zaman lafiyar da aka bayyana ranar Jumu’a na da aniyar bin matakan hadewa tsakanin rundunar sojin Sham da na mayakan Kurdawa. Amurka ta yi maraba da wannan a matsayin muhimmin mataki na tarihi da zai kawo hadin kai da sulhu a kasar Sham bayan da aka kwashe shekaru 14 ana yakin basasa.


