Rahotanni daga Taiwan sunce an sami girgizar kasa mai karfin maki 7 , wadda ya auku a birnin Yilan dake kudu maso gabashin gabar ruwan kasar, kamar yadda aka ji daga hukumar kula da yanayi a yankin, nan da nan dai ba’ sami rahotannin irin barnar da girgizar ta janyo ba.
Girgizar tana da zurfin kilomita 73 a ƙarƙashin kasa, wadda aka ji motsinta a duk ilahirin kasar, har gine gine suka girgiza ko ina babban birnin Kasar Taipei, gwamnati a kananan hukumomi dake babban birnin kasar ba su bada labarin wata barna mai tsanani ba, in banda yoyon iskar Gas da ruwa.
Mazauna garin Yilan sun fuskanci daukewar wutan lantarki na wani dan gajeren lokaci, kamar yadda kamfanin samar da wutan lantarki na yankin ya fada.


