Bom din ya Tashi ne lokacin sallar magariba a masallacin a Kasuwar Gomboru a Maiduguri a Bayan Gudanar da tafsiri a masallacin

Anyi Tafsiri kafin sallar magariba kuma masallacin yau ya cika makil amma Wani mazaunin Unguwar ya shaidawa Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana Ibrahim Mustapha cewa, yau anyi Tafsiri kuma masallacin ya cika da Mutane, Bayan Bincike ansamu Wani bom da bai tashi ba a masallacin, amma dai an killace Unguwar a halin yanzu.

Amma ma hukunta kamar Hukumar ‘yan Sanda da Rundunar operation hadinkai basuce komi ba game da lamarin a hukunce.


