Fatima Buhari, ‘yar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa mahaifinta ya taɓa zargin ana sa ido a asirce kan ofishinsa a Fadar Shugaban Ƙasa.
Ta ce wannan ya sa a wasu lokuta suke sadarwa ta hanyar rubuta saƙonni maimakon magana.
An bayyana hakan ne a cikin sabon littafi mai taken From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari, wanda Dakta Charles Omole ya rubuta kuma aka ƙaddamar da shi a Abuja.
Littafin ya nuna cewa jami’an tsaro sun taɓa gano wasu abubuwa da ba’a saba gani ba a ofishin da ɗakin kwanan Buhari yayin binciken tsaro.
Fatima ta ce yanayin da ke cikin Villa ya kasance mai tayar da hankali, inda ta nuna fargabar cewa an yi yunƙurin cutar da mahaifinta.
Ta ƙara da cewa halin Buhari na yafiya da imani ya sa bai yawaita fuskantar mutane ko kunyata su a bainar jama’a ba, ko da an ci amanar sa.
Rahoton ya kuma nuna damuwa kan yadda ake zargin wasu ƙungiyoyi masu ƙarfi (“cabal”) da samun damar yin irin wannan sa ido a cikin Fadar Shugaban Ƙasa mai tsaro.


