Wani babban jami’in Amurka ta fuskar tsaro Joe Kent, wanda shine shugaban cibiyar yaki da ta’addanci yayi murabus ranar talata, saboda yaki da Amurka ta kaddamar kan Iran, yana cewa Farisa bata zama ko ta kasance mai barazana kan Washington ba. Kent ya zama jami’in Amurka na farko a gwamnatin Trump wanda ya ajiye aiki saboda adawarsa da wannan yaki, wanda ya shiga mako na uku.
“Babu yadda za’ayi cikin hankalina in goyi bayan yakin da ake yi da Iran. Iran bata kasance wata barazana nan take ga kasar mu ba, kuma a fili yake mun fara wannan yakin ne saboda matsin lamba daga Isra’ila da masu kama mata kafa wanda suke da karfi,” Kent ya rubuta a wasikar da ya wallafa a dandalin sada zumunta.
Wasu kwararru suka ce, ana bukatar a gwada Amurka tana fuskantar barazana kai tsaye, kamin Amurka ta kaddamar da yaki karkashin dokokin kasa da kasa na kaddamar ma yaki.
Sai dai da take maida martani, sakatariyar yada labarai a fadar White House Caroline Leavitt a sanarwa da ta bayar, tace wasikar da Kent ya aikewa shugaba Trump tana kunshe da “rashin gaskiya,” domin a cewarta shugaba Trump ya bayyana karara cewa yana da bayanai da suka nuna cewa Iran tana shirin ta kaiwa Amurka hari.


