An Gudanar da addu’oi karshen Shekara a Masarautar Kaltungo dake jihar Gombe, a yayin kamallah bukin al’adu na Karamar Hukumar Kaltungo na shekarar 2025.

A jawabin sa Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammadu ya yabawa kokarin dukkan wanda suka bada gudunmawa tare da kira ga ‘yan Masarautar dasu samar da Makarantu domin inganta Ilimi da zummar yakar jahilci a yankin.

Sannan kuma ya bukaci inganta harkokin noma ta hanyar samar da kayan aiki na zamani.
Shima a jawabin sa Shugaban kwamitin tsara bukin na wannar Shekarar Mr. Muhammad Dantata Ndus ya godewa dukkan ‘yan Jarida da kafafen yada labarai da suka yayata Bukin na wannan shekarar.
Taron addu’oi’n wanda ya gudana a Fadar mai Kaltungo ƙarƙashin jagorancin Alhaji Saleh Muhammadu yasamu halartan manyan Malaman addinin Musulunci dana Mabiya addinin Kirista a Masarautar.

Daga cikin Malaman da suka halarta akwai Limamin Masallacin Fadar Gombe Barrister Aliyu Hammari Walama da Shugaban Jama’atul Nasrul Islam na jihar Gombe Alhaji Saleh Danburam, Pastor Babale Garus da shugaban CAN na shongom Pastor Enoch Timothy da Bishop Yilde Lapan.
Malaman addinin sunyi wa’azi tare da bukatar al’umma su hadakai su zauna lafiya da juna kuma kowa yayi addinin sa batare da tsangwama ba.
Masu wa’azin sun gudanar da addu’o’i na wanzuwar zaman lafiya a Masarautar Kaltungo, jihar Gombe dama Najeriya baki daya.


