Rahotanni daga hukumomin leken asiri na Amurka a baya bayan nan sunce dawuya Iran ta bude mashigin ruwan Hormuz cikin wani dan karamin lokaci ba, domin kama marar babbar hanyar jigilar makamashi ta duniya, itace kadai madafa da Iran take da ita kan Amurka, kamar yadda majiyoyi uku da suke da masanaiya dangane da batun suka fada.
Binciken ya nuna cewa Tehran zata ci gaba da tsuge mashigin domin tabbatar da tsadar makamashi a zaman wata hanyar matsawa shugaban Amurka Donald Trump, ya nemi mafita da daina yakin da bashi da farin jini wajen Amurkawa.
Haka nan rahoton ya nuna alamar cewa yakin da aka kaddamar da nufin karya karfin sojan Iran, maimakon haka kamar anyi mata tagomashi saboda ya kara mata martaba zata iya tayi barazana kan muhimmiyar hanyar zirga zirga ta cikin ruwa.
Trump yana biris da masu nuna cewa bude mashigin ruwan Hormuz zai yi wahala, wacce tana nan ne kashi 20 cikin dari na makamashi da duniya ta dogara akai yake bi. Jiya Jumma’a shugaban Amurka yace yana iya bada umarni ga sojojin Amurka su bude mashigin ruwan.
Ahalinda ake ciki kuma, jiragen dakon mai ta ruwa uku daga Oman, da wani jirgin kasar Faransa, da wani jirgin ruwan Japan mai dakon iskar gas sun ratsa ta mashigin ruwan Hormuz, wadda yake kara tabbatar da manufofin Iran na kyale jiragen ruwa daga kasashe da bata gaba da su su bi ta mashigin ruwan Hormuz.


