Ceto ɗaliban Neja ya dawo da natsuwa ga ƙasa, inji Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ya ce ceto ɗaliban da aka sace daga Makarantar Firamare da Sakandare ta St. Mary da ke Papyri, Jihar Neja, ya dawo da natsuwa da kwanciyar hankali ga iyalan su da ƙasa baki ɗaya.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Fadar Gwamnatin Jihar Neja domin yin godiya da kuma bayyana jin daɗin dawowar yaran lafiya.

Tawagar ta samu tarbar Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago.
Idris ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro, Gwamnatin Jihar Neja da al’ummar yankin ne ya taimaka wajen nasarar aikin ceton.
Ya ce: “Ceton waɗannan yara ya dawo da natsuwa ga iyalan su da kuma ga ƙasa baki ɗaya. Mun yaba da jajircewar jami’an tsaro, saurin ɗaukar matakin Gwamnatin Jihar Neja, da kuma haɗin kan al’umma wanda ya ba da damar samun wannan sakamakon.”
Ministan ya kuma jaddada cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki tsaron makarantu da kare ɗalibai da matuƙar muhimmanci.
Ya ƙara da cewa, “Dole ’ya’yan mu su samu damar yin karatu cikin tsaro. Gwamnatin Tarayya tana da cikakkiyar niyyar ci gaba da aiki tare da jihohi domin ƙarfafa tsaron makarantu, tare da tabbatar da cewa irin wannan ɓarna ga zaman lafiyar mu bai da wurin zama a ƙasar mu.”
A jawabin sa, Gwamna Bago ya gode wa Ministan bisa ziyarar, tare da yaba wa jami’an tsaro da al’ummomin yankin waɗanda suka taka rawa wajen ganin an sako ɗaliban.
Ya kuma jaddada cewa jihar za ta ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Tarayya domin ƙarfafa tsaro da zaman lafiya.


