Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot,
Dangantakar ta kara Tsamari ne bayan da Kocin Liverpool, Arne Slot ya cire jeren sunayen tawagar da za ta fafata da Inter Milan, ba tare da Salah ba, bayan dan wasan dan Ƙasar Masar yayi wasu kalamai masu tayar da hankali a kwanaki da suka haifar da rikici a Anfield.
An cire fitaccen dan wasan Liverpool Mohamed Salah daga tawagar da za ta fafata da Inter Milan a gasar zakarun Turai wadda hakan ya tada sabon rikici da kocin Arne Slot.

Tsohon dan wasan a Anfield, wanda ya taka rawar gani wajan samun nasarar Liverpool a gasar Premier a kakar wasa ta bara a karkashin Slot, yanzu yana fuskantar makoma mara tabbas a kulob din hakan na kara ruruwa wutan rikici a bayan fage.
Majiyoyin da ke kusa da ƙungiyar sun bayyana cewa rikicin da ya ɓarke tsakanin Salah da Slot ya wargaza dangantakar da ta daɗe tana tsakanin ɗan wasa da koci bayan wani rahoto daga Fabrizio Romano cewa za a iya cire ɗan wasan na Masar.
Hakan ta biyo bayan maganar da Salah ya yi bayan da aka ajiye shi a benci karo na uku a jere ciki harda wasan da Liverpool tayi da Leeds United, inda kalaman bai yi wa Slot daɗi ba, wanda hakan ya haifar da rashin jituwa da masu sharhi suka bayyana a matsayin “wanda ba zai iya gyaruwa ba.”
Wannan rashin jituwa ya yi tsanani har aka cire Salah daga tawagar Liverpool da za ta je Italiya don fafatawa da Inter Milan UCL, wanda hakan ke nuna sako a bayyane daga shugabannin ƙungiyar.
Duk da Salah ya atisaye da ‘yan uwansa, magoya bayan Liverpool suna mamakin wannan mataki, ganin yadda Salah ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasan ƙungiyar da kuma muhimmiyar rawar da ya taka a kakar wasansu ta Zakarun Turai.

Rashin ɗan wasan gaban na Masar ya haifar da manyan tambayoyi game da alkiblar ƙungiyar da kuma yadda suke shirin durkusar da hazakarsa a gaba.
Yayin da wannan labarin ke ci gaba da bayyana, magoya bayan Liverpool suna jira don sanin ko tauraron dan wasansu zai iya murmurewa daga wannan rikicin.


