Dubban mutane ne suka yi zanga zanga fadin kasar Australia ranar Litinin, domin nuna adawa da fara ziyarar da shugaban jeka nayika na Isra’ila Isaac Herzog yake yi a wasu biranen kasar, domin karfafa dangantaka da jajantawa yahudawan dake kasar bayan mummunar harin da aka kai musu a bara.
Herzogg ya kai ziyara Australia cikin makon nan, bayan da PM kasar Anthony Albanese ya gayyace shi bayan harin da aka kai kan taron yahudawa da suke bikin addinin su a gabar ruwan kasar ranar 14 ga watan Disamba bara, har maharan suka kashe mutane 15.
Ziyarar da shugaba Herzogg yake yi ta harzuka wasu mutane a kasar wadanda suke zarginsa cewa yana da hanu a kashe farar hula a Gaza. Kungiyoyi da suke goyon bayan Falasdinawa sun shirya zanga zanga a birane da garuruwa a duk kasar a yammacin ranar Litinin.
Dubban mutane ne suka hallara a wani dandali a birnin Sydney suna sauraron jawabai suna ambaton kalaman goyon baya ga Falasdinawa.


