A halin da ake ciki, ‘yan kallo na Kungiyar Tarayyar Tattalin Arziki ta Afirla ta Yamma, ECOWAS, da kuma Kungiyar Tarayyar Afirka AU, sun bayyana damuwa a game da juyin mulkin soja a Guinea-Bissau, da kuma kama jami’an hukumar zabe da aka yi.
A cikin wata sanarwar hadin guiwa da suka bayar, ‘yan kallon kungiyoyin biyu sun ce abin takaici ne cewa wannan sanarwa ta yin juyin mulki tazo a daidai lokacin da su wakilan na kasashen Afirka suka gama ganawa da dukkan manyan ‘yan takara biyu a zaben, inda kowannensu ya bada tabbacin cewa zai yi na’am da duk abinda jama’ar kasar suka yanke hukumci a kai.
Tawagar ‘yan kallon da ta kumshi tsohon shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, da tsohon shugaba Jacinto Nyusi na Mozambique, ta yi kira ga kungiyoyin yan kin da su dauki matakan da suka kamata na maido da yin aiki da tsarin mulki a kasar Guinea Bissau.
Sanarwar ta kuma yi kira ga sojoji da su sako jami’an hukumar zabe domin su kammala aikin da suke kan yi na tattarawa da sanar da sakamakon zaben da aka yi.


