Tsohon kocin Kamaru Marc Brys ya zargi shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kamaru (FECAFOOT) Samuel Eto’o, da tsoma baki a zaben ‘yan wasan Indomitable Lions da za su fafata a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta 2025,
Brys, wanda aka kora makonni kadan kafin fara gasar da aka tsara daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga Janairu, ya yi ikirarin cewa Eto’o ne yake Zaben ‘Yan wasa ba sabon kocin da aka nada David Pagou ne ya dauki nauyin tsara jerin ‘yan wasa na karshe ba.
Kocin dan kasar Belgium ya soki cire manyan taurari, ciki har da mai tsaron gidan Manchester United André Onana da kyaftin dinsa Vincent Aboubakar na dogon lokaci, yana mai bayyana ceresu a matsayin rashin adalci da kuma illa ga damar Kamaru a gasar.

Abubakar shi ne na biyu mafi yawan kwallaye a tarihin kungiyar kwallon kafa ta kasar, inda ya zura kwallaye 45 a wasanni 116.
“Eto’o ya cire manyan ‘yan wasa, kuma Jagorori, domin ya sa ka wanda yake so wannan a bayyane yake “in ji Marc.
Marc ya ce ta yaya za ku iya shiga gasa irin wannan ba tare da mai tsaron gida sananne a duniya ba, ko kuma ba tare da Aboubakar ba?

Waɗannan ‘yan wasa ne masu kwazo, waɗanda ke tsayawa tsayin daka ” in ji Brys a wata hira da wata kafar yada labarai
Brys ya ƙara da sukar halayen Eto’o, yana zargin tsohon ɗan wasan Barcelona da Inter Milan da cewa mai son kai ne.
“Duk wannan ba abin mamaki ba ne a gare ni wajan wanda ke son kai kuma yana tunanin shi ne ya Iya ,” in ji shi.


