Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci
Published: March 2, 2026 at 1:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa an kama wani ma’aikacin ɗakin girki na Fadar Aso Rock bisa zargin yunƙurin sa guba ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar da ke musanta labarin, inda ya bayyana cewa rahoton ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, babu wani ma’aikacin ɗakin girki na Fadar Aso Rock da aka kama, haka kuma babu wanda ya yi yunƙurin sa guba ga Bola Ahmed Tinubu.

“Babu wani ma’aikacin ɗakin girki na Aso Rock da aka kama. Babu kuma wani ma’aikacin da ya yi yunƙurin sa guba ga Shugaba Tinubu. A yi watsi da wannan labarin ƙarya da ake yaɗawa ta wani bidiyo,” in ji sanarwar.

Fadar ta buƙaci al’umma da su yi taka-tsantsan da labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tare da yin watsi da jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Afrika, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Shugaban Amurka Yace Sojojin Amurka Dana Iran Sunyi Taho Mugama

Karin Labarai Masu Alaka

An tura tsohon ministan Ilimin Nijar gidan yari saboda zargin aikata fyade ga wata daliba. Afrika
Tattaunawar Nukiliya Tsakanin Iran Da Amurka Yana Tasirin Akan Farashin Albarkatun Mai Amurka
An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Game Da Matsalar Tsaro A Najeriya Najeriya
Harin Makami Mai Linzami Da Rasha Ta Kai Yayi Barna Sosai A Ukraine Afrika
Farashin Danyen Mai Ya Fadi A Kasuwar Duniya Afrika
An Kashe Sojojin Ukraine Dubu 55 A Kasar Rasha Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci
  • Shugaban Amurka Yace Sojojin Amurka Dana Iran Sunyi Taho Mugama
  • Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani
  • Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi
  • Jirgi Marar Matuka Yayi Luguden Wutan A Abu Dhabi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Gwamnatin Trump Ta Karawa Iran Wasu Takunkumai Amurka
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
  • Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya Labarai
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.15.2025 Rediyo
  • Yanbindiga sun Kashe kimanin mutane 30 a yankin kayama ta Jihar kwaran Najeriya Najeriya
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasashen Cambvodia Da Thailand Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsaro
  • Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.