‘Amfani da ‘Yan Wasan Da Ba Su Cancanta Ba: FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca, Ta Sanar Da kwace mata Nasara a wasanni Uku Saboda Laifinsu
Hukumomin kwallon kafa na duniya sun ce a ranar Laraba, FIFA ta hukunta Malaysia da shan kaye a wasanni uku inda kowani wasan ya nuna an sha su 3-0 a yanzu saboda sanya ‘yan wasan da ba su cancanta ba, hukuncin da aka yanke na ƙarshe ke nan kan wannan lamari.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta ce an soke nasarar da Palestine da Singapore, da kuma kunnen doki da Cape Verde, duk a gida a wannan shekarar.
FIFA ta riga ta dakatar da ‘yan wasan ƙungiyar ƙasa bakwai ‘yan ƙasashen waje saboda rubuta takardu na jabu waɗanda suka yin ikirarin cewa asalinsu ‘yan ƙasar Malaysia ne.
Sau kuma hukumar FAM, wacce a da aka ci tararta dala $440,000, yanzu an sake hukunta ta da ƙarin dala $12,500.
Taron kwamitin ladabtarwa na FIFA a ranar Juma’a ya yanke hukuncin cewa “An ayyana Malaysia a matsayin wadda ta sha kashi da ci 3-0 a dukkan wasanni uku”, in ji FAM.
Binciken da ya gudanar ya nuna cewa babu ɗaya daga cikin wayannan ‘yan wasa da Malaysia tayi amfani da Hector Hevel, Jon Irazabal, Gabriel Palmero, Facundo Garces, Rodrigo Holgado, Imanol Machuca, ko Joao Brandao Figueiredo da ke da iyaye ko kakanni da aka haifa a Malaysia, wanda hakan ke nufin basu cancanci a zaɓi su a matsayin ɗan wasan ƙasar va.
FAM ta musanta duk wani laifi kuma ta yi alƙawarin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Sasantawa ta Wasanni.


