Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar
Published: February 20, 2026 at 1:35 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ministan harkokin wajen Guinea Bissau ya ce gwamnatin kasar ta tsaida binciken kiwon lafiya da gwamnatin Donald Trump ta dauki nauyinsa, da nufin auna tasirin da kuma abunda ka iya faruwa da wadanda aka yi wa allurar rigakafin shawara ko hepatitis B da turanci, da kuma yadda hakan yake kuma shafar wadanda suke fama da larurar setin kwakwalwa ko autism da turanci.

Guinea Bissau daya daga cikin kasashe matalauta a Afrika ta yamma, ‘yan kasar masu yawa suke da shawara. Sai dai binciken ya janyo suka matuka daga masana kimiyya, kungiyoyin kiwon lafiya na kasa da kasa, har ma shugaban hukumar kiwon lafiya na duniya Tedres Ghebereysus ya soki shirin da za’a bada allurar riga kafin ga rabin yara da aka haifa.

A cikin watan jiya ne Guinea Bissau ta dakatar da shirin sai bayan an sake nazari. Masu sukar lamirin shirin suka ce ana gwaje gwajen ne da nufin alakanta alllurar riga kafi da larurrar setin kwakwalwa, da ministan kiwon lafiya na Amurka Robert F. Kennedy karami, yake ta yayatawa, amma kuma masana kimiyya suka musanta matsayar da yake dauka.

Ministan harkokin wajen Guinea Bissau Jao Bernado Viera ya fada a hira da aka yi dashi a ranar talata cewa an rufe shirin, yace kwararru a tafarkin kimiyya da kuma senatocin Amurka sun soki lamirnsa.

Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Hukumomin Tsaron Kenya Sunce ‘Yan Kasar Suna Fafata Yaki Da Dakarun Rasha A Ukraine
Next Post: An Kaddamar Da Rigakafin Cutar HIV AIDS A Kasar Zimbabwe

Karin Labarai Masu Alaka

Alaka Na Cigaba Da Kamari Tsakanin Rwanda Da Barundi Labarai
Farashin Gangar Mai Yayi Gagarumar Fadi A Kasashen Duniya Labarai
Harin Ukraine Yayi Mummunan Barna A Rasha Afrika
Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
Kasar China Ta Daina Bada Bashi Da Dalar Amurka Sai Da Kudin Kasar Yuan Labarai
Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
  • AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya Wasanni
  • Wani Ya Yiwa ‘Yar Sa Mai Shekaru 8 Fyade A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump: Zamu Kawo Zaman Lafiya A Fadin Duniya Amurka
  • Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
  • ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Sun Kama Wasu Matasa da Ake Zargin Su Da Sara Suka  Labarai
  • Sakataren Gwamnatin Amurka Ya Bayyana Bawa Kungiyoyin Agaji Damar Kai Taimako Sudan Amurka
  • Amurka Da Iran Zasu Tattauna A Kasar Oman Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.