Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Asabar, ya yi jawabi ga sojojin rundunar Birget na 25 na Sojin Najeriya, inda ya bayyana goyon bayan jihar ga yakin da suke yi da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP.

Gwamnan, wanda ke jawabi a sansanin sojoji a Damboa, ya tausaya wa jami’an da sojoji, yana mai godiya ga dimbin sadaukarwar da suka yi da kuma kokarin da suke yi a kullum.
Ya yaba wa abin da ya bayyana a matsayin “Namijin kokarinsu da kuma sadaukarwar su” a yakin da ake yi don kare Jihar Borno da kuma kare fararen hula daga barazanar Boko Haram da kuma Islamic State West Africa Province (ISWAP).
Zulum ya ce, “A madadin gwamnati da mutanen jihar Borno, Mun zo Damboa don yi muku jaje kan koma bayan da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin abokan aikin ku.
Yace Wannan lamari ne mai ban takaici, kuma ina so in mika ta’aziyyata gare ku da iyalan dukkan jami’ai da ma’aikatan wannan runduna da suka rasa rayukansu yayin da suke gudanar da ayyukansu tare da addu’ar Allah yabawa wadanda suka ji rauni a fagen daga lafiya da wuri-wuri.
Ga wadanda daga cikinku wadanda har yanzu suna raye kuma suna cikin koshin lafiya, muna addu’ar Allah ya kare ku, ya ba ku hangen nesa da karfin aiwatar da ayyukanku yadda ya kamata, sannan muna yabawa da goyon bayan ku kuma muna so mu yaba muku.
Gwamnan ya samu tarba daga Kwamandan Rundunar Sojoji ta 25, Brigadier Janar Igwe Patrick Omokeh.
Ziyarar ta kasance wani ɓangare na rangadin Zulum ga al’ummomi a kudancin Borno.
A farkon yinin ranar, gwamnan ya gana da iyalai dake cikin alhini a Chibok, inda ya yi musu ta’aziyya game da asarar rayuka da dukiyoyi, ya kuma yi ta’aziyya da kuma jaje ga waɗanda suka rasa kadarori.
A lokacin taron a Chibok, gwamnan ya sanar da matakai na musamman don kare rayuka da dukiyoyi. Ya lura cewa gwamnatin jihar, tare da haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro, tana aiwatar da ƙarin matakai don kare al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali daga hare-hare.


