Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya ce barin jam’iyyar PDP da ya yi ya biyo bayan gazawar jam’iyyar wajen kare shi a rikicin siyasar jihar.
Fubara, wanda ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki a Fadar Gwamnati da ke Fatakwal, ya ce ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu ta tabbatar masa da cikakken goyon bayan da PDP ta kasa bashi.
Ya kuma tabbatar da komawarsa jam’iyyar APC tare da manyan magoya bayansa, yana mai cewa jam’iyyar ta ba shi kariya da goyon bayan da ake buƙata domin tsallake rikicin siyasar Rivers.
“Da ba don Shugaba Tinubu ya shiga tsakani ba, da babu Siminalayi Fubara a yau,” in ji shi, yana mai bayyana kudurinsu na mara wa Tinubu baya a tazarcen 2027.
- Sauya sheƙar Fubara yana ƙara sauya yanayin siyasar Rivers, tare da yiwuwar yin tasiri a zabukan 2027 masu zuwa.


