Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa an sace yara 48 ‘yan asalin jihar masu shekaru tsakanin biyu zuwa biyar, inda ya ce an kai su wasu sassan duniya kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito.
Inuwa Yahaya ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da rabon tallafin Abincin Ramadan a Gombe, inda ya nuna damuwa kan rashin tabbacin ko za a sake samun yaran lafiya.
Yace tsaro alhakin kowa ne, tare da buƙatar mazauna jihar su mara wa matakan gwamnati baya domin dakile barazanar da ke addabar zaman lafiya.
Gwamnan ya kuma ce dokar hana cinikin ƙarafa da takaita amfani da babura an ɗauke su ne domin inganta tsaro da rage satar ababen hawa.
Haka zalika, ya koka kan lalata kayayyakin more rayuwa, inda ya ce an taɓa kayayyakin wutar lantarki na Muhammadu Buhari Industrial Park da kuma madatsar ruwa ta Dadin Kowa Dam.
Ya ƙara da cewa mutane 70,000 ne za su amfana da tallafin Ramadan, tare da umartar kwamitin rabon kayayyakin da su tabbatar da gaskiya da adalci kuma Suyi rabon a cikin mako daya.


