Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Kano Zata Dauki Mataki Game Da Kisan Dorayi
Published: January 20, 2026 at 7:52 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴ aƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin alhini da girgiza.

Gwamnatin ta bayyana kisan a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi da rashin imani wanda ya girgiza zukatan al’ummar jihar tare da zama babban cin zarafi ga bil’adama da doka.

A cikin wata sanarwa da babban lauyan jihar kuma kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN ya ce bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Kano.

”Gwamnati na tare da iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa ba za a barsu su kaɗai ba a wannan mawuyacin lokaci,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta yaba wa rundunar ƴansandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakin bincike da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.

A cewar sanarwar, wannan mataki na nuna ƙudirin hukumomin tsaro na tunkarar aikata laifuka da dawo da amincewar jama’a ga tsaro da adalci.

Gwamnatin ta jaddada cewa za a gudanar da shari’ar cikin gaggawa da ƙwarewa ta hannun Ofishin Babban Lauyan jihar, inda za a kafa tawagar lauyoyi ta musamman domin tabbatar da adalci.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Gana Da Shugaba Tinubu
Next Post: Talauci Ya Ragu A Tsakanin Al’ummar Jihar Jigawa

Karin Labarai Masu Alaka

Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos Afrika
Iran Ta Rufe Sararin Samaniyar Ta Labarai
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Makaman Nukiliya Afrika
Kudin Man Fetur Ya Karu Da Kashi 10 Cikin 100 Afrika
Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi Labarai
Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shin Ko Ganawar Zelensky Da Macron Zata Haifar Da ‘Da Mai Ido? Labarai
  • Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
  • An Gudanar Da Jana’izar ’Yan Jaridan Da Suka Rasu A Jihar Gombe Labarai
  • Abba Kabir Yusuf Ya Koma Jam’iyar APC Siyasa
  • Tattalin Arzikin Najeriya Ya Farfardo Bisa Samun Wasu Sauye Sauye Labarai
  • Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya Tayi Kakkausar Lafazi Game Da Harin Maiduguri Afrika
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Makaman Nukiliya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.