Ta hanyar amincewa da hadin guiwa da kasar Amurka a bainar jama’a, kan harin da Amurkan ta kai ranar kirsimeti, Nigeria ta tsallake rijiya da baya wajen fuskantar harin sojin Amurka kai tsaye, wanda shugaba Donald Trump ya yi barazanar kaiwa wata daya da ya wuce.
Amma masana harkar tsaro sun ce babu tabbacin ko irin waddannan hare-hare zasu iya maganin ‘yan ta’adda da suka dade suna barazana ga mutanen yankin
Trump ya fada a shafin sa na Truth Social ranar Alhamis cewa dakarun Amurka sun kai farmaki ga kungiyar ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin Nigeria, bayan da gwamnatin Nigeria ta bukaci hakan, ya ce ‘yan ta’addan suna cin zarafin mabiya addinin kirista.
Ranar Jumu’a Trump ya ce harin da sojan Amurkan suka kaiwa ‘yan ta’adda da, da farko ranar Laraba ya kamata a kai shi, amma sai ya ce a dakata sai washegari.
Wani jami’in tsaron Amurka da ya nemi a boye sunan sa, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa An yi amfani da makamai masu linzami na Tomahawk ne, wanda aka harbo su daga jirgin ruwan yakin Amurka a tekun Guinea.
Fadar gwamnatin Nigeria a Abuja ta tabbatar da yarjewar ta ga kai harin, kamar yadda ministan harkokin kasashen waje Yusuf Tuggar ya fada ranar Jumu’a, cewa harin na hadin guiwa ne, kuma bashi da alaka da wani yanki.


