Wani hari da aka kai da jirgi mara matuki na drone a yankin Darfur na kasar Sudan ranar Laraba. ya kashe a kalla fararen hula 30 da suka hada da mata da yara, a yayin da suke halartar wani bikin aure, a cewar ofishin Majalisar Dinkin Duniya a jiya Alhamis.

Mai magana da yawun sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric, yace an gudanar da bikin auren ne a garin Kutum, a arewacin Darfur.
Kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam sun dora alhakin harin kan dakarun sojin Sudan.


