PM Britaniya Keir Starmer yayi magana da Yeriman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bn Salman, bayanda Iran ta kaiwa saudiyyan hari, yayinda rikici yake kara bazuwa a yankin, kamar yadda fadar gwamnatin Britaniyan ta fada ranar jumma’a.
“An tura karin jiragen yaki, da masu saukar ungulu, da kuma jirgin ruwa mai dakon jiragen yaki zuwa yankin, kuma a shirye Ingila take ta goyi bayan duk wani mataki na bada kariya ga daular Saudiyya, idan bukatar haka ta taso, Starmer ya gayawa Bn Salman.
Haka nan shugabannin biyu sun tattauna kan bukatar kara hadin kai wajen tattara bayanan sirri da da nufi ayyukan kariya da kuma farar hula


