Nasry Asfura, dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai ra’ayin mazan Jiya, a kasar Honduras wanda shugaban Amurka Donald Trump ke marawa baya, ya lashe zabe, kamar yadda hukumar zabe ta sanar ranar Laraba, fiye da mako uku bayan gudanar da zaben ranar 30 ga watan Nuwamba, wanda ya samu tsaiko, matsalolin na’ura da kuma zarge-zargen magudi.
Hukumar zabe ta kasar Honduras da aka fi sani da CNE, ta ce Asfura ya ci kashe 40.3 cikin 100 na kuri’u inda ya kayar da dan jam’iyyar liberal, Salvador Nasralla, wanda ya samu kashi 39.5 cikin 100 na kuri’un. Dan takarar jam’iyya me mulki, jam’iyya libre Rixie Moncada kuma ya zo na uku.


