Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

INEC: Akwai Yiwuwar Dage Zaben 2027 Saboda Azumi
Published: February 14, 2026 at 4:03 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta ce tana ci gaba da tuntuba kan jadawalin babban zaɓen 2027, bayan da aka nuna damuwa cewa ranar zaɓen ta yi daidai da watan Ramadan.

A wata sanarwa da Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Haruna, ya fitar, hukumar ta ce an tsara ranakun ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki na 1999 da dokar zaɓe ta 2022 da kuma ƙa’idojin INEC.

INEC ta sanya 20 ga Fabrairu, 2027 domin zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi zai gudana a 6 ga Maris, 2027.

Sai dai wasu ‘yan Najeriya, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, sun buƙaci a sake duba ranakun, suna mai cewa sun faɗa cikin watan azumi, wanda ka iya shafar yawan fitowar masu zaɓe.

Haruna ya ce hukumar na duba lamarin, kuma idan buƙatar hakan ta taso, za ta nemi matakin Majalisa domin tabbatar da gudanar da zaɓe mai haɗa kowa da kowa.

Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata
Next Post: Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana

Karin Labarai Masu Alaka

Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
Shugaba Trump Ya Amince Da Tsawaita Cinikayya Tsakanin Amurka Da Kasashen Afirka Afrika
Iran Da Amurka Zasu Cimma Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
Kasar Ukraine Ta Yabawa Tarayyar Turai Bisa Bata Tallafi Labarai
MDD: Fiye Da Farar Hula Metan 200 Suka Mutu A Sudan Afrika
Birtaniya Zata Fara Raba Rigakafin Allurar Cutar Sankara Kimiya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Mabiya Dariqar Tijjaniyya Sunfara Gudanar Da Addu’oi Saboda Tsare Sheikh Sani Khalifa Zariya Afrika
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Afrika
  • Hukumar Hasashen Kasuwanci Na Zargin Saida Bayanan Sirri Amurka
  • Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro. Najeriya
  • Sojin Saman Najeriya Sunyi Gagarumar Nasara A Yankin Borno Najeriya
  • Sojin Najeriya Da ‘Yan Ta’adda Sunyi Taho Mugama Najeriya
  • CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
  • Alkalan Wasannin Kwallon Kafa A Ghana Zasu Samu Inshora Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.