Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Iran Zata Kawo Karshen Yaki Da Isra’ila Da Amurka
Published: April 6, 2026 at 8:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A ranar Litinin Iran tace tana so a kawo karshen yakin da take tafkawa tsakanin ta da Isra’ila da Amurka na dindindin, ta kuma yi watsi da matsin lambar da ake mata na tayi gaggawar bude mashigin ruwa na Hormuz, ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta na wucen gadi, yayin da Amurka da Iran ke duba yadda za’a tsara kawo karshen yakin da akayi makonni biyar ana yi.

Iran ta aike da martanin ta, kan kudurin da Amurka ta bayar na kawo karshen yakin ta hannun kasar Pakistan, inda taki yarda da tsagaita wuta, tana mai jaddada bukatar kawo karshen yakin gaba daya, kamar yadda kafar yada labarai ta Iran ta IRNA ta fada a ranar Litinin.

Martanin da Iran ta bayar ya kunshi sharuda goma, wadanda suka hada da kawo karshen yake-yake a yankin Gabas ta tsakiya, yarjejeniyar tabbatar da wucewar jirage lafiya ta mashigin ruwa na Hormuz, cire takunkumin da aka kakaba mata, da kuma sake gina wuraren da aka rushe mata.

Shugaban Amurka Donald Trump da yayi barazanar luguden wuta kan Tehran idan ba’a cimma yarjejeniyar bude mashigin ruwa na Hormuz ba zuwa karfe takwas na daren gobe Talata ba, wato karfe 12 kenan agogon GMT, yayi watsi da kudurin na Iran, yana mai cewa wa’adin da ya bayar shine na karshe.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi A Edo
Next Post: Shugaban Amurka Yayi Barazanar Kulle Wani Dan Jarida

Karin Labarai Masu Alaka

Dakarun Sojin Amurka Sunfara Sauka A Najeriya Amurka
Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
Farashin Gangar Mai Yayi Gagarumar Fadi A Kasashen Duniya Labarai
Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza Labarai
‘Yan Tawayen Kasar Kwango Ne Suka Kai Hari Filin Jirgin Saman Kisangani Labarai
Birtaniya Ta Bukaci Israela Ta Janye Shawarar Fadada Iko Da Kogin Jordan Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga
  • Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi
  • Shugaba Trump Yayi Barazanar Tarwatsa Cibiyar Makamashin Iran
  • Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Ta Bukaci Duniya Ta Shirya Domin Fuskantar Tsadan Mai Amurka
  • Amurka Tasakawa Sojin Rwanda Takunkumi Afrika
  • An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka Amurka
  • An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro
  • Hukumomin Tsaron Najeriya Ne Suka Bukaci Amurka Ta Turo Musu Sojoji Amurka
  • Iran Ta Karyata Tattaunawa Da Washington Afrika
  • A Kowacce Rana Kasar China Tana Sayan Danyen Mai Ganga Dubu 600 Daga Kasar Venezuela Amurka
  • Gwamnatin Janhuriyar Nijar Ta Soke Lasisin Wasu Kamfanonin Dakon Mai Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.