Gabanin shigowar watan azumin Ramadan, Church of Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Sabon Tasha a Kaduna ta raba kayan abinci ga Musulmi sama da 1,000, makarantun Islamiyya na Tsangaya da kuma wasu ‘yan gudun hijira (IDPs), a wani mataki da ke ƙara ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.
An gudanar da rabon kayan ne a harabar Kano Road Central Mosque, inda Babban Faston Majami’ar, Dr. Yohanna Buru, ya bayyana cewa manufar shirin ita ce bunƙasa haɗin kai, juriya da zaman lafiya a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, tsawon shekaru 20 da suka gabata, Majami’ar na tallafa wa Musulmi marasa galihu da makarantun Tsangaya a jihohin Arewa biyar da kayan abinci a duk lokacin Ramadan, domin ba su damar gudanar da azumi da ibada cikin walwala.
Ya ce ana raba shinkafa, masara da sauran kayan masarufi, tare da tabarmi da butocin roba, tare da ƙarfafa wa waɗanda suka amfana da tallafin gwiwar yin addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ƙasa.
Fasto Buru ya kuma bayyana cewa, sakamakon tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki, ya tattara fastoci da limamai 50 domin gudanar da gangamin kwanaki bakwai tare da ‘yan kasuwa a kasuwanni, da nufin rage farashin kayan abinci domin sauƙaƙa wa al’umma a lokacin Ramadan.
Ya ƙara da cewa kowace shekara Majami’ar na taimakawa wajen biyan belin wasu fursunonin Musulmi, domin su samu damar yin azumi tare da iyalansu.
Haka kuma ya yaba da gudummawar da wata baiwar Allah Musulma, Hajiya Ramatu Tijjani, ke bayarwa duk shekara ga zawarawa da marayu a lokutan bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Babban Faston ya yi wa Musulmi a faɗin duniya fatan samun Ramadan mai albarka, tare da kira gare su da su ci gaba da yin addu’o’i domin dorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Da yake karɓar kayan a madadin masu buƙata ta musamman, Shugaban Ƙungiyar Masu bukata ta musamman a jihar Kaduna, Malam Hassan Lawal, ya bayyana matuƙar godiya bisa wannan tallafi, yana mai kira ga attajiran Musulmi da su ƙara zage damtse wajen tallafa wa marasa galihu da kayan abinci domin su samu damar mayar da hankali ga ibada.
Haka zalika, Shugaban Ƙungiyar Makafi ta Jihar Kaduna, Malam Tukur Zubairu, ya yaba da yadda ake tunawa da su tsawon shekaru 20 a kowane watan Ramadan, yana mai cewa Allah ne kaɗai zai saka wa Faston bisa wannan karamci da kulawa.
A nasa jawabin, Imam Ibrahim Musa, wanda ya yi magana a madadin makarantun Tsangaya a Kaduna, ya gode wa Fasto Yohanna Buru bisa wannan tallafi, tare da kira ga sauran masu hali da su yi koyi da wannan kyakkyawan misali na zaman tare cikin lumana.
Shi ma Murshidin Jama’atu Nasril Islam, Imam Ilyasu, ya bayyana wannan mataki a matsayin gagarumin abin a yaba, yana mai kira ga masu hannu da shuni da su riƙa fitar da zakka da sauran sadaka domin tallafawa Musulmi marasa galihu, musamman a wannan lokaci na azumin Ramadan.


