Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Jiragen Saman Yakin Najeriya Suka Gurgunta Yunkurin Juyin Mulki A Benin
Published: December 9, 2025 at 3:25 AM | By: Ibrahim Alfah Ahmad

Hukumomin Jamhuriyar Benin, sun fada jiya litinin cewa hare-haren da jiragen saman yaki na Najeriya suka kai sune suka gurgunta yunkurin juyin mulki a kasar, inda sojoji masu bore suka yi kokarin kama shugaba Patrice Talon.

Sojoji masu yunkurin juyin mulkin sun samu isa dab da Shugaba Talon, wanda ya gane ma idanunsa ba-ta-kashi tsakaninsu da masu gadinsa, kuma har sun iya suka kama wasu manyan hafsoshin soja guda biyu wadanda ba a sako su ba sai jiya litinin da safe.

Wadannan bayanan suna kumshe a cikin wata sanarwar da gwamnatin Jamhiriyar Benin ta wallafa game da yunkurin juyin mulkin, a bayan wani zaman majalisar ministocinta.

Sanarwar ta ce jiragen saman yakin Najeriya sun kai hare-hare suka lalata motocin yaki masu sulke na sojoji masu juyin mulkin, ba tare da sun kashe wani ba. Daga bisani, wasu zaratan sojoji daga kasar Cote D’Ivoire sun isa Cotonou, inda aka girka su domin daukar mataki ko da boren sojojin zai ci gaba.

Sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin sun fito daga sansanin soja na Togbin, inda tun kafin ketowar alfijir na ranar lahadi suka fara yada zango a gidan babban hafsan sojojin kasar, Janar Bertin Bada. An kashe matar janar din a gwabzawar da aka yi a wurin, amma hafsan ya samu ya tsere musu.

Sojojin sun samu suka kama babban hafsan sojojin kasa, Janar Abou Issa da Kanar Faizou Gomina, wadanda gwamnatin Benin ta ce an sako su daga bisani jiya litinin da safe a garin Tchaourou na arewacin kasar.

Masu yunkurin juyin mulkin, sun je suka kwace gidan telebijin na wani dan lokaci kafin a kore su, inda suka koma barikin Togbin, inda sojoji masu biyayya ga gwamnati da kuma jiragen saman yakin Najeriya suka yi ta far musu.

Har yanzu babu labarin inda Kanar Tigri Pascal yake, watau mutumin da aka ce shine jagoran masu yunkurin juyin mulkin.

Afrika

Post navigation

Previous Post: An Samar Da Dala Kusan Biliyan Biyu Don Yakar Polio
Next Post: Yarjejeniyar Britaniya Da Mauritius Kan Tsibiran Chagos Cin Zarafi Ne

Karin Labarai Masu Alaka

Ana Cigaba Da Kai Kayan Agaji Kasar Morocco Sakamakon Tsananin Hunturu Afrika
Jagoran Kasar Iran Yace Basa Bukatar Tallafin Kasar Amurka Afrika
Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf Afrika
Bahrain Ta Gabatar Da Kudurin Sulhu Ga MDD Afrika
Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farashin Danyen Mai Da Iskar Gas Ya Tashi Afrika
  • An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon Afrika
  • An Kashe Mutane 169 A Wani Harin Sudan Ta Kudu Afrika
  • ‘Yan Tawayen Kasar Kwango Ne Suka Kai Hari Filin Jirgin Saman Kisangani Labarai
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
  • Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
  • An Zargi Kasar Eritrea Da Cin Zarafin Sojojin Habasha Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.