Ma’aikatan Jirgin Ruwa 20 Sun Kuɓuta Daga Mutuwa Yayin Da Jirgin Rundunar Sojin Ruwa Ya Kama Da Wuta a jihar Cross River.
Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta ceto ma’aikata 20 daga wani jirgin ruwa, MV Chimba Express, da ya kama da wuta a hanyar ruwa ta Oron Calabar a jihar Cross River.
Aikin ceton ya gudana ne a ranar Litinin ta hannun jirgin NNS OSE, bayan kiran gaggawa da aka samu yayin da jirgin ke kan hanyar sa daga Gabon zuwa Calabar.
An ce jirgin na ɗauke da mutane 21, ciki har da ’yan Najeriya 14 da ’yan Kamaru bakwai.
Rundunar ta bayyana cewa Babban Injiniyan jirgin ya ɓace bayan da ya yi tsalle cikin ruwa, inda ake ci gaba da aikin bincike da ceto.
Jami’an sojin ruwa, tare da taimakon jami’an tsaro da masunta na yankin, sun yi nasarar kashe wutar tare da ceto sauran mutanen.


