Faransa tace zata bunkasa makaman Nukiliyar ta kuma zata kyale kawayenta a turai su zama masu masauki ga jiragen yakin na ruwanta da suke dauke da makaman Nukiliya a zaman ziyara ta rigakafi ko garkuwa, kamar yadda shugaban kasar Emmanuel Macron ya fada ranar Litinin, matakin da ya nuna babban canji kan manufofi ga Faransa da kuma turai baki daya.
Koda shike Faransa da Ingila duka suna da makaman Nukiliya, ga galibin kasashen turai sun dogara ne da Amurka domin kariya daga dukkan mai wata muguwar anniya, karkashin kunigyar tsaro ta NATO.
Amma ganin yadda shugaba Trump yake dasawa da Rasha dangane da yakin Ukraine, da kuma ganin hali da yake nunawa wadanda sune ainihin kawayen Amurka, hakan ya girgiza gwamnatocin kasashe da suke turai, har yasa wasu kasashen suka fara nuna sha’awar yadda Faransa zata kare su karkashin shirin Nukiliyarta.


