Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel
Published: February 9, 2026 at 10:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: February 10, 2026

A ranar Litinin kasashen Saudi Arabia, Jordan da kasashen Haddadiyar Daular Larabawa sun yi Allah wadai da yunkurin da Isra’ila take yi na saukakawa ‘yan kasar ta yadda zasu samu matsuguni a yankunan yammacin kogin Jordan da ke mallakin Palastine.

Shawarar da majalisar tsaron Isra’ila ta yanke ranar Lahadi, zai saukakawa yahudawa wajen siyen filaye a yankin, kuma zai bawa Isra’ila karin karfin iko a guraren da a bisa zato suna karkashin ikon Palasdinawa ne, a cewar wasu manyan ministocin Isra’ila 2.

Daya daga cikin ministocin dake da ra’ayin tsananin kishin kasa, ministan kudi Bezalel Smotrich, da yake sanar da hukuncin, ya ce gwamnatin sa zata ci gaba da rushe ra’ayin wanzuwar kasar Palestine.

Wani jawabi daga ministocin kasashen gabas ta tsakiya da sauran kasahen larabawa, da suka hada da Masar da Turkiya sun yi Allah wadai da wannan kuduri, da ya karya dokokin kasa da kasa, kuma zai kawo kalubale ga mafitar da ake so a samu na kowanne bangare ya mallaki kasar sa, da kuma wanzuwar zaman lafiya a yankin.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Ana Cigaba Da Samun Hare Hare Da Jiragen Marasa Matuki A Sudan
Next Post: Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC

Karin Labarai Masu Alaka

Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
Rundunar Hadinkan Saudiya Tayi Ikirarin Mayar Da Martani Ga ‘Yan Aware Labarai
Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba Labarai
Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Gabatar Da Gwajin Makami Mai Linzami Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
  • Tattalin Arzikin Kasar Botswana Zai Farfado Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar Afrika
  • An Kashe Sojojin Ukraine Dubu 55 A Kasar Rasha Afrika
  • Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi Najeriya
  • CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.