Danyen man fetur dake fitowa daga Afirka ta Yamma yana yin kwantai a kasuwannin mai na duniya, yayin da dillalai suke neman masu sayen man da za a yi lodi daga 26 ga watan nan na Disamba har zuwa watan janairu.
Dillalai da masana a wannan fannin sunce yawan danyen man fetur na Najeriya da Angola da yayi kwantai yanzu haka a kasuwa, ya samu ne a saboda samun mai dake da araha a wasu sassan amma farashin danyen mai na Brent ya fadi zuwa kasa da dala 60 kan ganga guda a karon farko tun cikin watan Mayu.
Ya zuwa yau alhamis, akwai ganga miliyan 20 na danyen man fetur na Najeriya da za a yi lodinsa cikin wannan wata na Disamba da watan Janairu mai zuwa wanda yayi kwantai an rasa mai saya.
Haka ma akwai lodi 5 zuwa 6 na danyen man fetur na kasar Angola na wannan wata da wata mai zuwa wanda shi ma yayi kwantai.
Masana harkokin mai suka ce ba a saba ganin irin kwantai na danyen man fetur na Afirka ta yamma ba, musamman ma a watan disamba, a saboda an saba sayar da shi watanni biyu kafin a yi lodinsa.
An yi kiyasin cewa a farkon wannan makon, akwai danyen man fetur ganga miliyan 40 na wadannan kasashen da yayi kwantai a kasuwa.


