Ana fargabar mutuwar aƙalla mutane 200 bayan jiragen yaƙin sojin Najeriya sun kai hari a wata kasuwar ƙauye yayin da suke bin mayaƙan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a arewa maso gabashin ƙasar a daren Asabar, kamar yadda wani kansila na yankin da mazauna wurin suka bayyana a jiya Lahadi.
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, yayin da take mayar da martani kan rahotannin da ke nuna fararen hula sun jikkata, ta ce a cikin wata sanarwa cewa ta kaddamar da sashen binciken hadurran da ke shafar fararen hula (Civilian Harm Accident and Investigation Cell) “domin nan take ya tafi wurin da abin ya faru don gudanar da bincike kan zargin.”
Tun da farko, rundunar sojin saman ta bayyana cewa ta kashe mayaƙan Boko Haram a yankin Jilli da ke jihar Borno.
Daga bisani, gwamnatin jihar makwabciyar ta Yobe ta ce a cikin wata sanarwa cewa an kai harin sama a yankin kusa da wata kasuwa inda masu saye da masu sayarwa suka taru.


