Kungiya Mabiya addinin kirista a Najeriya sun musanta ikirarin da sojoji suka yi na cewa sun kubutar da mutane 31 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kaduna, inda suka ce mutanen har yanzu suna nan a tsare.
Sojojin Najeriya sun fada ranar Lahadi cewa dakarun su sun kubutar da mutane farar hula, bayan da wasu ‘yan bindiga suka far ma wani coci a kauyen Ariko dake gundumar Kachia a jihar Kaduna, suka yi gaba da mutane, suka kuma hallaka wasu biyar.
Shugaban kungiyar kiristoci na CAN, reshen arewa Joseph Hayab, ya musanta cewa An kubutar da kowa. Yace ya san sojoji suna iya bakin kokarin su, amma ba daidai bane ace an kubutar da kowa, bayan ba haka bane.


